Ba Inyamurai suka kashe yan Arewa a Abia ba, kuyi hakuri: Ohanaeze ga al'ummar Arewa

Ba Inyamurai suka kashe yan Arewa a Abia ba, kuyi hakuri: Ohanaeze ga al'ummar Arewa

  • Ohanaeze Ndigbo tana bada hakuri ga daukacin al'ummar Arewa bisa abinda ya faru a jihar Abia
  • Kungiyar kare hakkin Igbon tace yan bakin haure sukayi aika-aika ba ainihin yan jihar ba
  • An hallaka akalla Hausawa takwas a harin da wasu yan bindiga suka kai kasuwar dabbobi a Abia

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta jajantawa al'ummar Arewa, Malaman addinin, Sarakunan gargajiyan Arewa, da kungiyar dattawan Arewa bisa kisan Hausawa a jihar Abia.

A jawabin da sakatare janar na kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya baiwa manema labarai a Kaduna, yace suna aika sakon ta'aiyya ga shugabannin arewa da wadanda sukayi rashin 'yanuwansu a abinda ya faru a Abia.

Kungiyar ta bayyana cewa ba yan kabilar Igbo bane, wau yan bakin haure ne.

Yace:

"Wadanda suka kai wannan harin azzaluman mutane ne, wadanda suka kashe yan Arewa ba Inyamurai bane. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa yan bakin haura ne kuma sun gudu jihohinsu."

Kara karanta wannan

Zamu hana kai Shanu jihar Legas, dss: Gwamnatin jihar Adamawa

"Mun jinjinawa kungiyar dattawan Arewa, kungiyar matasan Arewa, gamayyar kungiyoyin Arewa bisa bakin da suka sa don kawar da barkewar yaki musamman ramuwar gayya kan Igbo dake Arewa da kuma gwamnatin jihar Abia bisa kokarinta."

Ohanaeze ga al'ummar Arewa
Ba Inyamurai suka kashe yan Arewa a Abia ba, kuyi hakuri: Ohanaeze ga al'ummar Arewa Hoto: Mazi

Babu wanda ya isa ya hana Hausawa harka a kudu

Mazi Okechukwu Isiguzoro ya kara da cewa:

"Muna son bayyana cewa babu wanda ya isa ya hana yan Arewa harkar sayar da Shanu a kudu kuma muna watsi da barazanar IPOB na haramta kasuwar Shanu a kudu maso gabas."
"Inyamurai na harkokinsu a Arewa kuma babu wanda ke musguna musu, saboda haka kada wanda ya musgunawa wadanda ke harkoki a gabas."

Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia

Gamayyar kungiyoyin arewa (CNG) da na matasan arewa (AYCF) sun yi Allah wadai da harin da aka kai kan yan arewa a kasuwar shanu da ke jihar Abia wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka, sun ce ba za a lamunci hakan ba.

Kara karanta wannan

Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu da ke garin Omumauzor, karamar hukumar Ukwa ta yamma a jihar Abia a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, da misalin 11:35 na dare, inda suka kashe mutane takwas.

Yayin da suke martani ga harin a sanarwa daban-daban, kungiyoyin sun yi watsi da lamarin sannan sun yi kira ga gwamnatin jihar Abia da ta hukunta wadanda suka aikata ta’asar, Daily Trust ta rahoto.

Kakakin kungiyar CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya ce ya zama dole gwamnatin jihar ta gaggauta hukunta masu laifin sannan ya yi gargadin cewa arewa ba za ta kuma yarda da hare-hare mara tushe kan mutanenta da ke kudu maso gabas ko sauran yankin kasar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel