Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

  • Bayan shiga yajin Malaman jami'o'in Najeriya ranar Litinin, Malaman Poly ma na shirya daka nasu
  • Malaman sun bayyana cewa bayan watanni bakwai na yarjejeniya da gwamnatin tarayya, har yanzu ba'a cika musu alkawari ba
  • Gabanin wannan Malaman kwalejin ilimin (COEASU) kazalika sun bayyana niyyar bin sahu na jami'a

Kazaure - Kungiyar Malaman makaratun fasaha a Najeriya (ASUP) ta y kira ga mambobinta su shirya shiga yajin aiki saboda nan ba da dadewa ba za'a iya yin haka.

Shugaban ASUP, Mr Anderson Umezurike Ezeibe, ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga mambobin kungiyar a Hussain Adamu Federal Polytechnic, Kazaure, jihar Jigawa, rahoton DailyTrust.

` A cewarsa, gwamnatin tarayya bata cika wasu alkawurran da tayi musu ba a Yunin 2021.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata

Yace janye daga yajin aiki a 10 ga Yunin 2021 bisa yarjejeniyar da sukayi da gwamnati.

Kungiyar Malaman Poly ASUP
Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP Hoto: ASUP
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Anderson ya ce tun lokacin gwamnatin tarayya bata cika wasu alkawurranta ba.

Yace:

"Duk da dakatad da yajin aikin, har yanzu ba'a saki kudi (N15bn) na gyara ba tun bayan da Shugaba Buhari ya bada izinin a biya, hakazalka ba'a biya mafi karancin albashi ba."
"Har yanzu muna tattaunawa. Saboda haka shiga yajin aiki ne abinda ya halalta muyi idan gwamnati taki biyan bukatunmu."

Ya kara da cewa da yiwuwan majalisar zartaswar kungiyar ta yanke shawara a ganawarta da za tayi a Maris a Mubi, jihar Adamawa.

Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata

Adamu Adamu, ministan ilimi, ya ce matakin yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) na wata daya "abin mamaki ne"

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Ya ce ba laifin gwamnatin tarayya ba ne idan har ba a cimma matsaya ba bayan tattaunawa da dama tsakanin bangarorin biyu.

Ministan ya yi wannan magana ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Adamu ya ce ASUU ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne ba zato ba tsammani a dai dai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel