Naɗin Farfesa Da Aka Yi Wa Pantami Ya Saɓa Ƙa'ida, A Sake Duba Wa, In Ji Kungiyar Tsaffin Ɗaliban FUTO

Naɗin Farfesa Da Aka Yi Wa Pantami Ya Saɓa Ƙa'ida, A Sake Duba Wa, In Ji Kungiyar Tsaffin Ɗaliban FUTO

  • Kungiyar tsofaffin daliban jami’ar tarayya ta fasaha da ke Owerri, FUTO, ta ce bai dace hukumar makarantar ta bai wa Pantami farfesa ba
  • Ta bayyana hakan ne ta wata takarda wacce sakataren kungiyar, Kingsley Azuaru da shugaban ta, Ndubuisi Chijioke suka sanya hannu
  • Kungiyar ta goyi bayan kungiyar malaman jami’a ta kasa, ASUU wacce ta shawarci hukumar FUTO akan sauya ra’ayinta na ba shi matsayin

Kungiyar Tsofaffin Daliban Jami’ar Tarayya ta Fasaha da ke Owerri, FUTO, ta ce bai dace hukumar makarantar ta ba Isa Ali Pantami farfesa a jami’ar ba, Daily Trust ta ruwaito.

Ta bayyana wannan ra’ayin nata ne ta wata takarda wacce sakataren kungiyar na tarayya, Mr Kingsley Azuaru da shugaban kungiyar, Ndubuisi Chijioke, suka sanya hannu.

Kara karanta wannan

Shiga yajin-aikin ASUU ke da wuya, Malaman FCE sun soma barazanar rufe makarantu

Naɗin Farfesa Da Aka Yi Wa Pantami Ya Saɓa Ƙa'ida, A Sake Duba Wa, In Ji Kungiyar Tsaffin Ɗaliban FUTO
Kungiyar Tsaffin Ɗaliban FUTO: Naɗin Farfesa Da Aka Yi Wa Pantami Ya Saɓa Ƙa'ida, A Sake Duba Wa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Dama kungiyar malaman jami’a, ASUU ta bayyana rashin dacewar FUTO ta ba shi matsayin farfesa inda ta shawarce ta da ta kara dubawa.

Kungiyar ta tsame kanta daga cikin masu shirya liyafar karrama Pantami

Kamar yadda takardar ta zo:

“Kungiyar tsofaffin daliban FUTO ta tsaya a matsayin ta na batun rashin dacewar ba Pantami farfesa.
“Kungiyar ta amince da matsayar ASUU da ta nuna rashin dacewar lamarin kuma NEC ma bata aminta da batun farfesancin Pantami.
“Sakataren kungiyar na tarayya ya tabbatar da yadda kungiyar ta ke tsaya akan batun rashin dacewar ba Pantami farfesa.”

Kungiyar ta kara da cewa abin ban takaici be ace kungiyar dattawan tsofaffin daliban jami’ar tana shirin hada liyafa wacce take da niyyar nuna karrama ministan.

Kara karanta wannan

Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

Kungiyar ta kara da cewa ba ta da masaniya dangane da kungiyar dattawan ta. Don a iya sanin ta, kungiyar a dunkule take wuri guda babu rarrabuwa.

A cewar kungiyar, shirya dinar da sunanta kamar keta haddin ta ne

Takardar ta kara da tsame kungiyar a shirin liyafar, inda tace bata da masaniya kuma NEC ta tsaya akan cewa amfani da sunan kungiyar wurin shirya liyafar kamar keta haddin ta ne.

Ta ce NEC din kungiyar bata dauki nauyi ko kuma ta kashe sisin kwabon ta ba wurin shirya liyafar. Haka zalika NEC din tana kara tsame mambobin kungiyar tsofaffin daliban daga shiga cikin shirye-shiryen liyafar.

NAN ta ruwaito yadda malamai da dama suka soki nadin Pantami, ministan sadarwa a matsayin Farfesa.

Shugabancin ASUU na kasa ta shawarci hukumar FUTO da ta janye matsayin farfesan da ta ba Pantami don a cewar ta, bai cancanta ba.

Sai dai hukumar FUTO tana nan akan bakar ta na tabbatar da nadin Pantami a matsayin farfesa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel