Shiga yajin-aikin ASUU ke da wuya, Malaman FCE sun soma barazanar rufe makarantu

Shiga yajin-aikin ASUU ke da wuya, Malaman FCE sun soma barazanar rufe makarantu

  • Kungiyar COEASU ta fara nuna alamun za a tafi yajin aiki a makarantun FCE idan har aka yi wasa
  • Dr. Smart Olugbeko ya ce an dauki lokaci gwamnatin tarayya ta na raina musu hankali a kan hakkokinsu
  • Shugaban COEASU na kasa baki daya, Smart Olugbeko ya bayyana cewa kwanan nan za ayi taron NEC

A ranar 15 ga watan Fubrairu 2022 jaridar Tribune ta bayyana cewa an ji kungiyar COEASU ta makarantun horas da malamai ta na yin barazanar yajin-aiki.

Kungiyar ta COEASU ta bakin shugabanta, Dr Smart Olugbeko ta gargadi gwamnatin tarayya cewa za su tafi yajin-aiki idan ta yi wasa da alkawarin da ta dauka.

Dr. Olugbeko ya ce tsakanin Agusta zuwa Disamban 2021, sun yi ta zama da manyan jami’an gwamnatin tarayya domin magance sabanin da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Shugaban na COEASU ya zargi gwamnatin Buhari da raina masu hankali saboda shirun da suka yi, ya ce dole a tabbatar da yarjejeniyar 2009 ko su yi yajin-aiki.

Gwamnati ta na kukan ta na fama da karancin kudin da za ta biya bukatun nan. Kungiyar kuma ta ce kusan makarantun ne ke daukar rabin dawainiyar kansu.

Malaman FCE
Makarantar FCE Yola Hoto: schoolings.org
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin shugaban COEASU

“Gwamnati ta nuna mana tsantsar rashin girmamawa saboda dattakun mu wajen magance matsalar, hakan ya sa ake yi mana kallon mu na da rauni.”
“Don haka, kungiyar ta na kira ga gwamnatin tarayya tayi maza ta fara dabbaka yarjejeniyar da aka cin ma a 2009, ta fito da N15bn na gyaran makarantu.”
“A ‘yan makonni masu zuwa, za mu kira taron NEC domin daukar matakin da dokar kasuwanci ta yarje, idan gwamnati ta gaza yin abin da ya dace.”

Kara karanta wannan

Matashi Ya Garzaya Masallaci Bayan Ya Lashe miliyan N38 A Caca Da Ya Buga Da N800, Bidiyon Ya Yadu

Ana samun kalubale a FCEs

Daily Trust ta rahoto kungiyar COEASU ta na karin haske da cewa kakaba malamanta da aka yi a karkashin tsarin biyan albashi na IPPIS su na kawo cikas.

Haka zalika gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ki fitar da N15bn da ake bukata domin a bunkasa makarantar koyar da harkar malanta a kasar nan.

Za a sasanta da ASUU?

A jiya da yamma aka ji cewa bisa dukkan alamu Gwamnati za ta yi hobbasa, ta dakatar da yajin aikin ‘Yan ASUU, a bude Jami’o’i domin yara su cigaba da karatunsu.

Duk-duka ASUU ba ta wuce kwanaki uku da fara yajin-aiki ba, amma an ji Ministan ilmi ya fara kokarin yin abin da aka yi shekara ana sauraron gwamnatin kasar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel