Ba 'yan IPOB ne ke son ganin bayan ka ba: Adamu Garba ya yi martani ga Abba Kyari

Ba 'yan IPOB ne ke son ganin bayan ka ba: Adamu Garba ya yi martani ga Abba Kyari

  • Dan takarar shugaban kasa, matashi Adamu Garba ya fito ya magantu kan matsayin Abba Kyari, inda yace babu wasu da ke son ganin bayansa
  • Adamu Garba ya bayyana cewa, Abba Kyari ya aikata laifi, kuma ya kamata ya amsa laifinsa ba tare da bata lokaci ba
  • Idan baku manta ba, Abba Kyari ya zargi 'yan kungiyar IPOB/ESN da son ganin bayansa saboda yadda ya addabe su

Adamu Garba, wani tsohon da takarar shugaban kasa na APC ya bukaci Abba Kyari da ya daina zargin haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, ko kuma jami’an tsaronta, watau Eastern Security Network a kan halin da yake ciki.

A rahoton da ‘yan sanda suka fitar a ranar Laraba, wanda jaridar Punch ta samu kwafinsa, Kyari ya zargi IPOB da ESN da tsoma shi cikin bala'i.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

Adamu Garba ya shawarci Kyari
'Yan IPOB/ESN ke son ganin baya na: Adamu Garba ya yi martani ga batun Abba Kyari | Hoto: Adamu Garba II
Asali: Facebook

Wani bangare na rahoton ya kara da cewa,

“Jami’in bai musanta karya ka'idojin kafafen sada zumunta na ‘yan sanda ba. Jami’in (Kyari) ya bayyana cewa ‘Kokari ne na bata masa suna daga ‘yan kungiyar IPOB/ESN da suka yi yunkurin halaka shi saboda yadda ya addabe su a yankin Kudu maso Gabas."

Martanin Adamu Garba

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Garba ya ce:

“Ya kamata Abba Kyari ya daina zargin IPOB ko ESN duk da mun san ko su wane ne, amma ya kamata ya zargi kansa domin ya bayyana a matsayin mai laifi kamar na kowa kuma ya kamata a dauke shi a haka."

Abba, wanda ‘yan sanda suka dakatar a watan Yulin da ya gabata, bisa zarginsa da alaka da dan damfarar Intanet, Hushpuppi, yana hannun hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Ahmad Musa ya yiwa tsohon dan kwallon da ya talauce kyautar N2m

Ka ci ka yi hani'an: Shehu Sani ya shawarci Abba Kyari kan yadda ake zaman gidan kaso

A wani labarin, an shawarci kwamandan hukumar leken asiri ta IRT da aka dakatar, DCP Abba Kyari, da kada ya tafi yajin cin abinci a magarkamar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA).

Wannan nasiha mai dauke shawari ta fito ne daga bakin wani tsohon dan sanata, Shehu Sani, ta shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu.

Sani ya lura cewa magarkama a Najeriya ba a tausayi ko rarrashin fursunonin da suka yanke shawarar kin cin abinci, ya kara da cewa mutane kamar shi ba su da wani zabi illa su ci abinci su yi hani'an yayin da suke cikin sel.

Asali: Legit.ng

Online view pixel