Ka ci ka yi hani'an: Shehu Sani ya shawarci Abba Kyari kan yadda ake zaman gidan kaso

Ka ci ka yi hani'an: Shehu Sani ya shawarci Abba Kyari kan yadda ake zaman gidan kaso

  • An shawarci DCP Abba Kyari a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu da kada ya shiga yajin cin abinci yayin da yake tsare a hannun hukumar NDLEA
  • Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ne ya bai wa Kyari shawari kyauta a shafin sada zumunta
  • Sani ya ce shi da wasu mutanen da suka tsinci kansu a baya a irin wannan hali ba su tsaya wata-wata ba, sun ci sun sha a magarkama

An shawarci kwamandan hukumar leken asiri ta IRT da aka dakatar, DCP Abba Kyari, da kada ya tafi yajin cin abinci a magarkamar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA).

Wannan nasiha mai dauke shawari ta fito ne daga bakin wani tsohon dan sanata, Shehu Sani, ta shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Kwamared Shehu Sani ya shawarci Kyari
Ka ci ka yi hani'an: Shehu Sani ya shawarci Abba Kyari kan yadda ake zaman gidan kaso | Hoto: @ShehuSani

Sani ya lura cewa magarkama a Najeriya ba a tausayi ko rarrashin fursunonin da suka yanke shawarar kin cin abinci, ya kara da cewa mutane kamar shi ba su da wani zabi illa su ci abinci su yi hani'an yayin da suke cikin sel.

Daga ganin maganganun Shehu Sani, kamar dai yadda aka saba gani, cikin zolaya ya ba wa Kyari wannan shawarar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Kyari kada ya ki cin abinci, ya ci abinci kawai. Sel din Najeriya ba su da tausayi kan yajin cin abinci. Saboda haka muma mu ke ci duk lokacin da muka fada ciki. Amma bayan ka ci, za ka iya nuna kamar baka ci ba kawai."

Harkallar kwaya: Abba Kyari ya yi fallasa, NDLEA ta je kotu neman ci gaba da tsare shi

A wani labarin, jaridar Punch ta ruwaito cewa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar tare da wasu 'yan tawagarsa mutane hudu na iya ci gaba da zama a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA).

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

A cewar jaridar, hukumar ta garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta sanar da kotun aniyar ta na tsare wadanda ake zargin sama da awanni 48 da aka kayyade.

Da take zantawa da wata majiya mai tushe a hukumar, Punch ta bayyana cewa Kyari ya yi wasu bayanai da za su kai ga kara bincike don haka hukumar ta NDLEA ba za ta iya gurfanar da shi a gaban kuliya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel