Shekaru 6 kenan ina dakon soyayyar Ahmed Musa, Budurwa ta fallasa sirrin zuciyarta

Shekaru 6 kenan ina dakon soyayyar Ahmed Musa, Budurwa ta fallasa sirrin zuciyarta

  • Wata budurwa ta bayyana kaunar da ta dade ta na yi wa dan kwallo Ahmed Musa inda ta yi shekaru shida ta na dakon soyayyarsa
  • Budurwar mai zama a Kano, ta ce a baya ba ta ko kula samari saboda soyayyar dan kwallon amma daga bisani ta hakura aka saka mata rana
  • Ta bukaci duk wanda ya san Ahmed Musa da ya sanar masa cewa akwai mai sonsa a Kano kuma ta na son ganinsa ko sau daya tak a rayuwarta

Allah ne ke saka soyayyar dan Adam a zuciyar abokan halitta. Wata budurwa mai shekaru ashirin da hudu ta bayyana tsananin kaunar da ta ke wa Ahmed Musa.

Budurwar ta aika da sakonta ne ga @diaryofnorthernwoman inda ta ke bayyana tsananin kaunar da take yi wa fitaccen dan wasan kwallon kafar.

Kara karanta wannan

Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki, za ta haife shi

Shekaru 6 kenan ina dakon soyayyar Ahmed Musa, Budurwa ta fallasa sirrin zuciyarta
Shekaru 6 kenan ina dakon soyayyar Ahmed Musa, Budurwa ta fallasa sirrin zuciyarta. @diaryofnorthernwoman
Asali: Instagram

Ga yadda wallafar tace:

"Salam Malama ya aiki, ya fama da jama'a? Malama na rasa ta inda zan fara. Ni dai Allah ya jarabceni da son Ahmed Musa dan kwallo tun ina shekaru goma sha takwas. Ba na kula kowa. Duk wanda yace yana sona tsanar sa nake saboda ni hankalina na kan Ahmed Musa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Son maso wani koshin wahala. In takaice miki zance, yanzu dai Malama na cika shekaru ashirin da hudu, kuma son nasa sai abinda ya karu. Da na ga babu sarki sai Allah, yanzu dai an saka ranata da wani.
"InshaAllah aure na May amma wallahi Malama har kuka nake ina tausayin kaina. Abinda ya fi bani mamaki bai sanni ba amma kullum kara shiga raina ya ke yi. Ina mai tabbatar miki da cewa wallahi Malama da son bawan Allah nan zan mutu."

Kara karanta wannan

Ta Musamman ce: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar jama'a baki bude

Budurwar ta bukaci idan da wanda ya san dan wasan kwallon kafan da ya sanar masa cewa akwai masoyiyarsa a Kano. Ta na son sa fiye da komai kuma ta na son ganinsa ko sau daya burinta ya cika kuma hankalinta ya kwanta.

Kamaru: Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500

A wani labari na daban, Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya gwangwaje wani masallacin Juma'a da ke Garoua a kasar Kamaru da tallafin $1,500 bayan idar da sallar Juma'a, Punch Sports Extra ta ruwaito.

Masallacin wanda ya ke kusa da sansanin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya a Garoua, shi ne inda 'yan wasan ke sallah a kowacce rana tun bayan isar su yankin arewacin kasar Kamaru a ranar 5 ga watan Janairu.

Punch ta ruwaito cewa, ana sa ran wannan tallafin zai taimaka wa malaman masallacin wurin kammala ginin, wanda har yanzu ake kan yi.

Kara karanta wannan

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

Asali: Legit.ng

Online view pixel