Sojoji sun farmaki mafakar 'yan bindiga, sun hallaka kasurgumin shugaban 'yan bindiga Dogo-Umaru da wasu 41

Sojoji sun farmaki mafakar 'yan bindiga, sun hallaka kasurgumin shugaban 'yan bindiga Dogo-Umaru da wasu 41

  • Dakarun rundunar sojojin sama sun farmaki mabuyar yan bindiga a jihar Katsina
  • Sojojin sun yi nasarar hallaka Dogo Umaru, kasurgumin dan ta’adda mai biyayya ga Bello Turji
  • Hakazalika sun yi nasarar kashe wasu yan ta'adda 41 da ke aiki a karkashinsa

Katsina - Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai hari ta sama inda suka kashe Dogo Umaru, kasurgumin dan ta’adda mai biyayya ga Bello Turji. Harin ya kuma hallaka akalla wasu yan bindiga 40.

PRNigeria ta rahoto cewa hukumar soji ce ta yi umurnin kai harin ta sama bayan an tabbatar da Dogo Umaru tare da mukarrabansa sun aiwatar da wasu munanan hare-hare a kauyen Magama da ke karamar hukumar Jibia (LGA) ta jihar Katsina.

Daya daga cikin hare-haren bayan nan da suka kai ya yi sanadiyar mutuwar DPO din Magama, yayin da wani soja ya ji rauni.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

Sojoji sun farmaki mafakar 'yan bindiga, sun hallaka kasurgumin shugaban 'yan bindiga Dogo-Umaru da wasu 41
Sojoji sun farmaki mafakar 'yan bindiga, sun hallaka kasurgumin shugaban 'yan bindiga Dogo-Umaru da wasu 41 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Dogo Umaru da mayakansa suna kai hare-hare a kauyukan da ke kewaye daga wata makaranta da ke kusa wato makarantar Firamare ta Tsamben Dantambara, wadda ta dade da zama kufai, rahoton Thisday.

Sojoji sun zafafa hare-harensu a mabuyar yan bindiga

Sai dai kuma, an tattaro daga wata majiya ta soji cewa an tura jiragen yaki Katsina domin su yi maganin yan ta’adda.

Majiyoyi na mazauna kauyen da ke kusa da kauyen Tamben Babare sun bayyana cewa yan ta’adda 42 aka shafe a harin da sojin sama suka kai, ciki harda Dogo Umaru.

Rahoton ya kuma kawo cewa wani jami’in leken asiri na rundunar sojin Najeriya ya ce dakarun soji da wasu jami’an tsaro sun zafafa kai hare-hare a sansanoni daban-daban a yankin Arewa maso Yamma a yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Yan bindiga sun kashe DPO da Hafsan Soja a sabon hari a Jibia

A baya mun kawo cewa tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kuma kai hari karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina da daren Talata, 8 ga watan Febrairu, 2022.

TVCNews ta ruwaito cewa yan bindigan sun hallaka DPO na ofishin yan sandan Magamar Jibiya da kuma wani hafsan Soja.

Hakazalika an ruwaito cewa wani kwamanda Soji ya jikkata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel