Cigaban Matasa: Gwamnatin Nijar Ta Tura Tawaga Zuwa Kano Domin Nazari Kan Tsare-Tsaren Gwamnatin Ganduje

Cigaban Matasa: Gwamnatin Nijar Ta Tura Tawaga Zuwa Kano Domin Nazari Kan Tsare-Tsaren Gwamnatin Ganduje

  • Ministan Koyar da sana'o'i na Jamhuriyar Nijar, Kassoum Mamane Moctar, a ranar Talata ya ce kasarsa ta gamsu da tsare-tsare da ayyukan da gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ke yi don cigaban matasa
  • Ministan ya ce nasarorin da gwamnatin na Kano ta samu a bangaren matasan yasa Nijar ta tura tawaga zuwa Kano domin yin nazari kan tsare-tsaren koyar da matasa sana'oi'
  • Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa ta gano cewa cigaban matasa ne ginshikin cigaba da kawar da ayyukan laifi shi yasa ta mayar da hankali a bangaren

Kano - Ministan Koyar da Sana'o'i na Jamhuriyar Nijar, Kassoum Mamane Moctar, a ranar Talata ya ce kasarsa ta gamsu da tsare-tsare da ayyukan da gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ke yi don cigaban matasa.

Ministan ya ce nasarorin da gwamnatin na Kano ta samu a bangaren matasan yasa Nijar ta tura tawaga zuwa Kano domin yin nazari kan tsare-tsaren koyar da matasa sana'oi', rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa bayan tafiyar Buhari Belgium

Cigaban Matasa: Gwamnatin Nijar Ta Tura Tawaga Zuwa Kano Domin Nazari Kan Tsare-Tsaren Gwamnatin Ganduje
Gwamnatin Kano za ta yi hadin gwiwa da Jamhuriyar Nijar don cigaban matasa. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Moctar ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata yayin da ya kai wa Gwamna Ganduje ziyara a gidan gwamnatin Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar da babban sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan Kano, Hassan Musa Fagge, ya fitar ta ce Ministan ya kara da cewa tsare-tsaren na cigaban matasa da gwamnatin Kano ta fitar abin koyi ne.

Martanin Ganduje

A bangarensa, Gwamna Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce gwamnatin jihar ta gano cigaban matasa shine ginshikin cigaba hakan yasa ta ke bawa tsare-tsaren matasan muhimmanci.

A cewarsa:

"Tallafawa matasa yana da matukar muhimmanci domin yana hana zaman kashe wando da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuka."

Gwamnan ya bawa tawagar ta Nijar tabbacin cigaba da hadin kai da goyon baya, yana mai cewa ziyarar da suka kai cibiyoyin tallafawa matasan shaida ne da ke nuna hadin gwiwa da ke tsakanin Najeriya da Nijar musamman Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel