Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu

Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno na shirin inganta rayuwar likitoci da sauran ma'aikatan jinya a jiharsa
  • Zulum yayni ziyarar da ya kai garin Gamboru a karamar hukumar Ngala, ya yiwa ma'aikatan jinya alkawarin cewa zai inganta jin dadinsu da albashinsu
  • Gwamnan wanda ya jinjinawa ayyukan ma'aikatan lafiyan, ya ce zai amince da albashin da zai yi daidai da tsarin biya na kungiyar agaji na kasa da kasa

Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yiwa likitoci da sauran ma’aikatan jinya alkawarin cewa gwamnatinsa za ta inganta jin dadinsu tare da duba albashi da ya dace da ayyukansu.

Zulum ya bayar da tabbacin ne a yayin ziyarar da suka kai garin Gamboru a karamar hukumar Ngala, tare da Sanata Kashim Shettima, inda suka kai kayan agaji daga ranar Lahadi zuwa Talata, Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Katsina ta haramta kungiyar Yan-Sa-Kai a fadin jihar

Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu
Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu Hoto: NewsPort Nigeria
Asali: UGC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Isa Gusau ya saki a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu mai taken ‘kwanaki biyu a Gamboru: Zulum, Shettima sun yiwa yan gudun hijira 60,803 rabon abinci da kudi.

Gwamnan wanda ya ziyarci babban asibitin gwamnati a garin Ngala, cibiyar kiwon lafiya a garin Gamboru, bayan ya kammala aikin bayar da agajin, ya yaba ma ma’akatan lafiya kan sadaukarwa da jajircewarsu.

Yayin da yake zantawa da likitoci, Zulum ya sanar da cewar zai amince da albashin da zai yi daidai da tsarin biya na kungiyar agaji na kasa da kasa wanda zai ja hankalin likitoci don su yi aiki a Ngala.

Gwamna Zulum Alheri ne ga al'ummar duniya gaba daya, Sanata Kashim Shettima

Kara karanta wannan

A hukumance: Daga karshe ASUU ta yi bayani dalla-dalla, ta shiga yajin aiki

A gefe guda, tsohon Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya mika godiyarsa ga Gwamna Babagana Umara Zulum, bisa rabon kayan abinci da kudi ga yan gudun hijra a mazabarsa.

Sanata Shettima ya bayyana cewa da kansu suka rabawa mutane sama da dubu sittin kayan abincin cikin kwanaki biyu.

A jawabin da Legit Hausa ta samu daga wajensa, Shettima ya ce Gwamna Zulum alheri ne ga al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel