Shugabar Alkalan jihar Zamfara ta kafa kwamitin bincike kan mataimakin gwamna, Mahdi Gusau

Shugabar Alkalan jihar Zamfara ta kafa kwamitin bincike kan mataimakin gwamna, Mahdi Gusau

  • Biyayya ga umurnin majalisar dokokin jihar Zamfara, Shugabar Alkalan Zamfara ta kafa kwamitin bincike kan Mahdi Gusau
  • Alkali Kulu ta nada mutane bakwai matsayin mambobin kwamitin kuma ya bukacesu suyi gaskiya
  • Zaku tuna cewa yan majalisar dokokin jihar 18 sun rattafa hannu a tsige mataimakin gwamnan jijar

Shugaban Alkalan jihar Zamfara, Mai Shari'a Kulu Aliyu, ta kafa kwamitin mutum bakwai don gudanar da bincike kan tuhume-tuhumen da majalisar dokokin jihar ke wa mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Gusau.

Mai Shari'a Kulu Aliyu ta rantsar da kwamitin ne ranar Litinin kuma ta nada tsohon Alkali, Tanko Soba, matsayin shugaban kwamitin, rahoton ChannelsTV.

Mahdi Gusau
Shugabar Alkalan jihar Zamfara ta kafa kwamitin bincike kan mataimakin gwamna, Mahdi Gusau Hoto: Mahdi Gusau
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa zata fara bawa masu juna biyu N5,000 a wata

Ayyukan kwamitin a cewarta sun hada da bincike kan tuhumar almundahana, ci da ofis, saba kundin tsarin mulki da kuma yin abubuwan da basu dace ba.

A cewarta, kundin tsarin mulki ya daura mata nauyi a matsayin Alkalin Alkalan jihar ta nada kwamitin.

Ta yi kira ga mambobin kwamitin suyi aiki tare kan zargin da akewa mataimakin gwamnan.

Yan majalisa 18 cikin 22 sun amince a tsige mataimakin gwamnan Zamfara

Mutum 18 cikin 22 na mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara sun amince da kudirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Wannan ya faru ne kwanaki uku bayan majalisar ta aike masa da sakon tuhume-tuhumen da ake masa.

Dan majalisa na jam'iyyar PDP, Salihu Usman (Zurmi ya gabas), kadai ne wanda bai amince a tsige Mahdi Gusau ba.

Majalisar tace za'a yi masa bincike ne bisa laifukan saba sasshe na 10 da 191(1), (2) (a)(b)(c) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel