Yan majalisa 18 cikin 22 sun amince a tsige mataimakin gwamnan Zamfara, sun umurci Alkali ya fara bincike

Yan majalisa 18 cikin 22 sun amince a tsige mataimakin gwamnan Zamfara, sun umurci Alkali ya fara bincike

  • Majalisar dokokin jihar Zamfara ta fara zaman tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau
  • Majalisar na tuhumar mataimakin, wanda 'da ne ga tsohon Ministan tsaro, Janar Aliyu Gusau, da wasu laifuka
  • Yan majalisar sun ittifakin a tsige Mahdi Gusau amma sai Alkalin jihar ya gudanar da bincike kan tuhume-tuhumen da dake masa

Gusau, jihar Zamfara - Mutum 18 cikin 22 na mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara sun amince da kudirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Wannan ya faru ne kwanaki uku bayan majalisar ta aike masa da sakon tuhume-tuhumen da ake masa.

A zaman ranar Alhamis, mambobin majalisa uku basu halarta ba, rahoton Ptimes.

Dan majalisa na jam'iyyar PDP, Salihu Usman (Zurmi ya gabas), kadai ne wanda bai amince a tsige Mahdi Gusau ba.

Kara karanta wannan

An garkame dan majalisar wakilan tarayya kan almundahanar N185m

Kakakin majalisan, wanda shine Alkalin kirgen ba kada kuri'a ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan majalisa
Yan majalisa18 cikin 22 sun amince a tsige mataimakin gwamnan Zamfara, sun umurci Alkali ya fara bincike
Asali: UGC

Bayan haka, majalisar ta umurci Alkalin Alkalan jihar, Kulu Aliyu, ya kafa kwamitin kaddamar da bincike kan tuhume-tuhumen da ake yiwa mataimakin gwamnan, riwayar Channels.

Majalisar tace za'a yi masa bincike ne bisa laifukan saba sasshe na 10 da 191(1), (2) (a)(b)(c) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

A raba ma kowa, zamu fara zaman tsige mataimakin gwamna: Kakakin Majalisar Zamfara

Dazu kun kawo muku cewa kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Magarya, ya umurci magatakardan majalisar, Shehu Anka, ya rabawa dukkan yan majalisa takardar fara shirin tsige mataimakin gwamna, Mahdi Gusau.

A cewar jawabin da mai magana da yawun majalisar, Mustafa Kaura, ya saki, ya bayyana cewa an yi hakan bisa sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

A raba ma kowa, zamu fara zaman tsige mataimakin gwamna: Kakakin Majalisar Zamfara

Kaakin, a cewar jawabin, ya bayyana umurnin a zaman majalisan ranar Laraba domin baiwa sauran yan majalisa daman karanta laifukan da ake tuhuman mataimakin gwamnan da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel