Fani-Kayode ya maka tsohuwar matarsa a kotu kan kiransa da mai karamin azzakari da yunkurin halaka shi

Fani-Kayode ya maka tsohuwar matarsa a kotu kan kiransa da mai karamin azzakari da yunkurin halaka shi

  • Precious Chikwendu, tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen saman, Femi Fani-Kayode ta gurfana a gaban kotu
  • Fani-Kayode ya maka ta kotu kan zarginta da kiransa da mai karamin azzakari kuma ta yi yunkurin halaka shi da sabuwar budurwarsa
  • Ya kara da bayyana cewa, sun yi amfani da yanar gizo wurin wallafa karairayi a kansa, inda ta ce ya na duka tare da lalata da 'yan aikinsa

FCT, Abuja - Tsohuwar matar ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, Precious Chikwendu, a ranar Litinin an gurfanar da ita a gaban wata kotun tarayya da ke Abuja kan zargin yunkurin halaka tsohon mijinta.

'Yan sandan sun gurfanar da Chikwendu a gaban Mai shari'a Inyang Ekwo kan zargin yunkurin kisan kai, Daily Nigerian ta ruwaito.

A karar mai lamba FHCABJ/CR/1/2022 wacce kwamishinan 'yan sandan babban birnin tarayyan ya shigar a kan Chikwendu da wasu mutum 3, an ce tsohuwar matar ta yi yunkurin soka wa Fani-Kayode wuka a ranar 24 ga watan Nuwamban 2018 a Asokoro.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: An ji harbe-harben bindiga yayin da rikici ya ɓarke tsakanin mambobin NURTW

Fani-Kayode ya maka tsohuwar matarsa a kotu kan kiransa da mai karamin azzakari da yunkurin halaka shi
Fani-Kayode ya maka tsohuwar matarsa a kotu kan kiransa da mai karamin azzakari da yunkurin halaka shi. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Sauran wadanda aka gurfanar tare da Chikwendu sun hada da Emmanuel Anakan, Prisca Chikwendu da Osakwe Azubuike yayin da sauran ba a kamo su ba, Daily Nigerian ta ruwaito.

A zargi 13 da aka shigar, wadanda ake zargin ana tuhumarsu ne da laifuka da suka hada da hantara, yukurin kisan Fani-Kayode da yunkurin kashe wata Lauretta wanda hakan yasa ta bar mu'amala da Fani-Kayode.

Ana zarginsu da yin amfani da yanar gizo wurin aika sakonni cin zarafi da niyyar hantara, bata sunan tsohon mijinta.

Ana zarginsu da hada shaidun karya wadanda suka haifar da tashin hankali inda suka ce Fani-Kayode ya na duka tare da lalata da ma'aikatan gidansa.

Ana zargin Chikwendu da amfani da shafin ta na Facebook wurin bayyana Fani-Kayode da "mai karamin azzakari" kuma a ranar 7 ga watan Disamban da ta gabata, an zarge ta da wallafa karya kan cewa tsohon ministan ba shi da kuzari kuma ba shi ne mahaifin yaranta hudu da ta haifa a gidansa ba.

Kara karanta wannan

Evans ya yi fallasa mai ban mamaki game da Abba Kyari da yaransa

Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su wadanda abun hukuntawa ne a karkashin sashi na 392 na dokokin Penal Code.

Mai shari'a Ekwo ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 27 Afirilu, 28 Afirilu da 29 Afirilu.

Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, tana son karbar 'ya'yansu

A wani labari na daban, tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigon jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, Precious Chikwendu ta maka tsohon mijinta a gaban kotu da bukatar karbar 'ya'yan da suka haifa.

Precious ta maka Fani-Kayode a gaban wata babban kotun tarayya dake Abuja inda take bukatar karbar 'ya'yanta hudu da suka haifa yayin da suke tare, amma a bar mahaifinsu ya dinga zuwa ganinsu, The Nation ta wallafa.

Matar mai son Fani-Kayode da duk wasu mukarrabansa su kiyayi kwace mata 'ya'yanta ta karfi da yaji, ta bukaci kotun da ta sa tsohon ministan ya dinga biyanta N3.438 miliyan duk wata domin kula da yaran tare da wasu kudi na daban domin karatunsu da sauran bukatunsu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP 25 sun nitse a kogin Marte yayin da suke guje ma harin sojoji

Asali: Legit.ng

Online view pixel