'Karin bayani: An ji harbe-harben bindiga yayin da rikici ya barke tsakanin mambobin NURTW

'Karin bayani: An ji harbe-harben bindiga yayin da rikici ya barke tsakanin mambobin NURTW

  • Kazamin rikici ya barke tsakanin bangarori biyu na kungiyar direbobin kasa NURTW a Agbado karamar hukumar Alimosho a Legas
  • Mutanen unguwa sun firgita sun rika tsere wa suna boye wa bayan sun ji karar harbe-harben bindiga sakamakon fadar da aka yi saboda karbar tikiti
  • Daga bisani kwamishinan yan sanda na Jihar Legas ya tura jami'ai daga wurare daban-daban zuwa Agbado inda suka kwantar da tarzomar

Rikici ya barke a unguwar Agbado a karamar hukumar Alimosho a Jihar Legas a ranar Juma'a da safe a yayin da bangarori biyu na kungiyar direbobi ta Najeriya, NURTW, suka kacame da fada a yankin.

Wasu da abin ya faru a gabansu sun tabbatarwa The Punch cewa masu ababen hawa da mutanen da ke wucewa a hanya sun tarwatse don su tsira da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa.

Yanzu-Yanzu: An ji harbe-harben bindiga sakamakon rikici da ya barke tsakanin mambobin NURTW
Rikici ya barke tsakanin yan NURTW a Legas, an ji karar harbin bindiga. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

An kuma ji harbe-harben bindiga a yayin rikicin da ya faru saboda karbar tikiti a tashohin mota.

Abinda Rundunar Yan Sanda ta ce game da lamarin

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Amma, ya ce an tura jami'an yan sanda zuwa wurin da abin ya faru.

Ajisebutu ya ce:

"Rikici ne tsakanin bada tikiti ya janyo muguwar rikici tsakanin bangarori biyu na NURTW a Kola Bus Stop da kewaye.
"Jami'an yan sanda masu sintiri daga Alakuko, Agbado, Ijaiye-Ojokoro da kuma wasu daga hedkwata aka tura unguwar bisa umurnin kwamishinan yan sanda, Abiodun Alabi.
"Hankula sun kwanta a yanzu. Babu barazanar rasa rayyuka ko dukiyoyi a yanzu, duba da cewa yan sanda suna can suna sintiri a unguwar."

Kara karanta wannan

An yi jana'izar DPOn yan sandan da yan bindiga suka kashe a Jibia

A baya-bayan nan mambobin kungiyar direbobi ta NURTW karkashin jagorancin Musiliu Akinsanya da aka fi sani da MC Oluomo sunyi rikice-rikice a baya-bayan nan.

The Punch ta rahoto yadda gwamnatin Legas, a makon da ta gabata ta dakatar da ayyukan NURTW a Idumota bayan wani rikici da aka yi a ungunwar.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel