Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, tana son karbar 'ya'yansu

Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, tana son karbar 'ya'yansu

- Tsohuwar matar Fani-Kayode, Precious Chikwendu ta maka tsohon ministan a gaban kotu

- Ta bukaci karbar 'ya'yan da suka haifa 4 tare da kuma N3.438 miliyan duk wata don kula dasu

- A karar, ta bada labarin yadda ya dinga dukanta tare da zaginta a aurensu mai shekaru shida

Tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigon jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, Precious Chikwendu ta maka tsohon mijinta a gaban kotu da bukatar karbar 'ya'yan da suka haifa.

Precious ta maka Fani-Kayode a gaban wata babban kotun tarayya dake Abuja inda take bukatar karbar 'ya'yanta hudu da suka haifa yayin da suke tare, amma a bar mahaifinsu ya dinga zuwa ganinsu, The Nation ta wallafa.

Matar mai son Fani-Kayode da duk wasu mukarrabansa su kiyayi kwace mata 'ya'yanta ta karfi da yaji, ta bukaci kotun da ta sa tsohon ministan ya dinga biyanta N3.438 miliyan duk wata domin kula da yaran tare da wasu kudi na daban domin karatunsu da sauran bukatunsu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kutsa garinsu ministan 'yan sanda, sun sheke 1 tare da sace matar babban limami

Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, ta bayyana cin zarafin da ta fuskanta
Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, ta bayyana cin zarafin da ta fuskanta. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Ta bayyana cewa yaran hudu da basu kai shekaru 6 ba a duniya suna cikin damuwa tun bayan da aka kwacesu daga hannunta a ranar 2 ga watan Augustan 2020. Ta kara da cewa bata saka su a ido ba sama da watanni bakwai.

A karar mai lamba CV/372/2021 wacce lauyanta E. D. Moi-Wuyep ta shigar, Precious ta bada bayani dalla-dalla yadda Fani-Kayode ya dinga cutar da ita da kuma dukanta a aurensu mai shekaru shida kacal.

Bayan kiran shari'ar a ranar Juma'a a gaban Mai shari'a Sylvanus Oriji na babban kotun da ke Apo a FCT, alkalin ya gano cewa Fani-Kayode ya ji sammacin amma yace bai same shi ba.

Mai shari'a Oriji ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Maris, lokacin da wanda ake kara ya samu sammacin.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kutsa garinsu ministan 'yan sanda, sun sheke 1 tare da sace matar babban limami

A wani labari na daban, jiragen sama da ke samar da makamai tare da abinci ga 'yan bindiga shine babban dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta hana jiragen sama bi ta jihar Zamfara, an gano hakan a ranar Laraba.

Baya ga haka, ana amfani da jiragen saman wurin safarar zinarin da aka haka ba bisa ka'ida ba a jihar.

Gwamnatiin tarayya ta haramtawa jiragen sama bi ta jihar Zamfara a ranar Talata bayan taron da aka yi na tsaron kasa. Ta kara da haramta dukkan hakar ma'adanai na jihar har sai baba ta gani, The Nation ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng