Bayanai: Yadda Abba Kyari ya bamu cin hancin $61,400 don mu saki hodar Iblis 25kg, dilan kwaya ne: NDLEA

Bayanai: Yadda Abba Kyari ya bamu cin hancin $61,400 don mu saki hodar Iblis 25kg, dilan kwaya ne: NDLEA

Hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi a Najeriya tayi bayani filla-filla yadda ta gano dakataccen DCP na yan sandan, Abba Kyari, yana safarar kwayoyi.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin, ya ce Abba Kyari mamban kungiyar masu safarar kwayoyi daga Brazil zuwan Habasha zuwa Najeriya.

Babafemi yace Kyari ya tuntunbi wani jami'in hukumar a Junairun 2022 da a saki wasu hodar iblis da aka kama.

Ga dogon jawabin:

"Bari in yi bayani filla-filla kan abinda ya faru. Lamarin ya fara ne ranar Juma'a, 21 ga Junairu, 2022, lokacin DCP Kyari ya kira wani jami'in NDLEA dake Abuja misalin karfe 2:12 na rana. Lokacin da jami'in ya sake kira bayan mintuna biyu, Kyari yace yana son zuwa don ganinsa, don tattauna wani lamari bayan Sallar Juma'a."

Kara karanta wannan

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

"Kyari ya yarda kuma suka shirya wajen haduwa da jami'in kuma yayi bayani. Hafsoshin Jami'in sun damke wasu masu safarar kwayoyi da suka shigo Najeriya daga Habasha, da kilo 25 na hodar Iblis, a cewarsa."

"Sai ya kawo shawarar cewa a bashi kilo 15 na hodar, sannan a ajiye kilo 10 don hukunta wadanda aka kama da hodar a Enugu. Amma zai bada wani hodar Iblis na bogi domin kilo 15 don kada a gane an cire. Sai ya bukaci jami'in ya yiwa abokan aikinsa bayani."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Misalin karfe 11:05 na safiyar Litinin, 24 ga Junairu, bayan hukumar ta baiwa jami'in izinin ya cigaba da biyewa Abba Kyari, sai suka fara waya a WhatsApp tsawon rana. Shi kuma hafsan yace abokan aikinsa sun amince ayi sauyin."

"Sai Kyari ya kara cewa zai baiwa jami'an NDLEA kudi don a sake rage kilo 5 cikin 10 na sahihin da ke hannun NDLEA, saboda ya rage kilo 5 kacal. Tunda ana sayar da kilo daya a N5m, kudin kilo 5 zai zama N35m, kuma farashin dala a ranar 24 N570/$, zai bada $61,400."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m

"Sai ya (Kyari) hanzarta jami'in ya gaggauta shirya abin da Kwamdanda NDLEA na Abuja don a fito da kwayoyin da wadanda aka kama daga hannunsu a Abuja. Amma a lokacin yana Legas."

"A ranar 25 ga Junairu, Abba Kyari yace zai turo kaninsa don ya kai kudin yayinda su NDLEA zasu saki wadanda aka kama, amma jami'inmu yaki yarda, yace lallai sai da Abba Kyari zai hadu. Zai jirashi ya dawo daga Legas."

"Misalin karfe 5:23 na yamma, Kyari ya koma Abuja kuma ya gana da jami'in a inda suka hadu a baya."

"Kyari ya nuna masa yadda zasu gane hodar iblis na kwarai da za'a kaiwa NDLEA, za'ayi musu digo da jan kala. Dalilin haka shine don kada a gwada jabun hodar . Sai ya turo hotunan. A tsarinsa, idan aka gwada sahihin hodar na kilo 5 a gaban wadanda aka kama, babu bukatar gwada sauran, marasa kyan."

Kara karanta wannan

Jerin gaskiya 12 da baku sani ba game da ɗan sanda Abba Kyari da aka damke

"Sai ya taho da kudin kilo 5 na NDELA da yayi alkawarin basu idan aka sayar, kudin $61, 400. Amma sai jami'in mu yace su shiga mota ya bashi kudin. Kuma motar na jibge da na'urar daukar bidiyo da magana."

"Mun gayyaci DCP Abba Kyari ofishin NDLEA don yayi bayani ranar Alhamis, 10 ga Febrairu. Amma har yammacin ranar Juma'a, 11 ga Febrairu, bai amsa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel