Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

  • Hedkwatar 'yan sandan Najeriya ta sanar da sunayen abokan harkallar Abba Kyari wurin safarar kwayoyi tsakanin kasashe a duniya
  • Jami'an NDLEA sun yi ram da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus a filin sauka da tashin jiragen sama na Akian Ibiam da ke Enugu
  • Bincike karkashin umarnin sifeta janar na 'yan sanda ya bayyana cewa akwai wasu jami'an NDLEA 2 a filin jirgin da ke rufa musu asiri tun 2021

FCT, Abuja - A ranar Litinin, hedkwatar 'yan sandan Najeriya ta bayyana sunayen wadanda ake zargi da hada kai da DSP Abba Kyari da wasu 'yan sanda hudu wurin shigo da miyagun kwayoyi cikin kasar nan.

Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA a ranar Litinin ta bayyana ta na neman Abba Kyari da tawagarsa, rahoton Premium Times ya bayyana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

'Yan sanda daga bisani sun damke wadanda ake zargi tare da mika su hannun hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyin domin cigaba da bincike.

Mataimakin kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da hakan a Abuja cewa akwai wasu jami'an NDLEA da ke da hannu a harkallar miyagun kwayoyin.

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi
Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce 'yan sandan sun aiwatar da bincike mai tsanani yayin da hukumar NDLEA ta aika musu da bukatar a ranar 10 ga watan Fabrairu.

"Kamar yadda dokokin aikinmu ya nuna, sifeta janar na 'yan sanda ya bayar da umarnin bincike mai tsauri na cikin gida kan zargin.
“Binciken farko ya ruwaito cewa abokan harkallar kwayoyi da ke safararsu tsakanin kasashe su ne Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus, wadanda aka cafke a filin sauka da tashin jiragen sama na Akanu Ibiam a ranar 19 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Jerin gaskiya 12 da baku sani ba game da ɗan sanda Abba Kyari da aka damke

"An damke wadanda ake zargin bayan isowarsu daga Addis Ababa ta jirgin kamfanin Ethiopia a jirgi mai lamba ET917.
"Bayan cafke su ne aka samu wani abu mai yanayin gari wanda ake zargin hodar ibilis ce."

Adejobi ya ce an mika mutum biyun da ake zargi hannun hukumar NDLEA a ranar 25 Janairu.

Ya ce sakamakon binciken cikin gidan wanda sifeta janar na 'yan sanda ya bada umarni, an gano hannun wasu jami'an IRT a harkar.

Premium Times ta ruwaito cewa, kakakin ya ce bincike ya nuna cewa jami'an suna wata harkalla ta rashawa wacce ta hakan ne ake karantsaye ga dokokin sannan a saki wadanda ake zargi da kuma abinda aka kama su da shi.

"Bayan haka, binciken 'yan sanda ya nuna cewa masu safarar miyagun kwayoyin na kasa da kasa suna da alaka mai karfi da wasu jami'an NDLEA.
"Shahararrun masu safarar miyagun kwayoyin tsakanin kasa da kasan sun bayyana cewa suna da alaka mai kyau tsakaninsu da jami'an NDLEA kuma sun tura musu hotunansu tun kafin su iso saboda su gane su.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

“Dabarar ita ce su samu damar wucewa salin alin sannan su fita daga filin jirgin saman da kwayoyin da suka shigo da su," ya kara da cewa.

Kamar yadda shahararrun masu safarar miyagun kwayoyin suka sanar, sun dade suna wannan alakar da jami'an NDLEA din da ke filin jirgin sama na Akanu Ibiam tun shekarar 2021.

Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama shugaban tawagar hukumar leken asiri ta IRT, DCP Abba Kyari da aka dakatar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa, an kama shi ne tare da wasu mutane hudu ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.

An kama Kyari ne sa’o’i kadan bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta bayyana cewa tana neman sa bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel