Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara

Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara

  • Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun ceto wasu mutum biyar da sukakwashe kwanaki takwas a hannun masu garkuwa da mutane
  • Mutum biyar din da aka ceto 'yan asalin karamar hukumar Bangi ne na jihar Niger kuma an same su ne a dajin Dansadau da ke Maru
  • 'Yan sandan sun ce an samo mutanen da aka ceto ne yayin samame da jami'an suka kai dajin Dansadau

Jami'an tsaro sun ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su wuraren dajin Dansadau a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara.

Wadanda aka yi garkuwan da su 'yan asalin jihar Neja ne a Kontagora da yankin karamar hukumar Bangi, TVC News ta ruwaito.

Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara
Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

TVC News ta ruwaito cewa, jami'an 'yan sanda ne suka ceto su bayan kwana takwas a hannun miyagun.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

Yayin zantawa da manema labarai a hedkwatocin 'yan sanda na Gusau, Muhammad Shehu ya ce, an ceto wadanda aka yi garkuwan dasu ne yayin bincike da samame a cikin dajin Dansadau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara
Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

A cikin su akwai wani dan shekara hamsin da dan shekara sha takwas.

A cewar 'yan sandan, an zanta da su, kuma za a mika su ga iyalan su.

Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara
Hotunan mutum 5 da 'yan sanda suka ceto daga miyagu a dajin Dansadau da ke Zamfara. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

Tsakanin watan Janairu zuwa yanzu, 'yan sandan Zamfara sun ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke liman, wasu 32, sun sace mata da yara kan kin biyan N40m haraji

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun halaka sama da rayuka talatin, sun yi garkuwa da wasu mata a hari mabanbanta a ranar Juma'a duka a jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An sace suriki da 'yan uwan miji yayin taron sulhunta mata da miji

Yankunan da aka kai farmakin sun hada da Nasarawar mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina a karamar hukumar Bungudu da kauyen Nasarawa da ka karamar hukumar Bakura.

Zamfara kamar sauran jihohin arewa maso yamma, ta na fama da rashin tsaro. Al'amuran 'yan bindigan kullum kara kamari su ke yi.

Dubban jama'a aka kashe kuma 'yan bindigan sun yi garkuwa da mutane masu yawa a yankin, lamarin da ya kara gaba har jihar Niger tun shekarar 2021.

A makonni uku na shekarar 2022, a kalla mutum 486 'yan ta'adda suka halaka a fadin Najeriya, rabi daga ciki kuwa duk a jihohin arewa maso yamma ne da jihar Niger.

Asali: Legit.ng

Online view pixel