Ba ku isa ba: Mai mota ya haukacewa gidan mai yayin da aka sayar masu ruwa da sunan mai

Ba ku isa ba: Mai mota ya haukacewa gidan mai yayin da aka sayar masu ruwa da sunan mai

  • Wani dan Najeriya ya koka bayan da yace an sayar masa da ruwa a wani gidan mai da ke yankin Ijebu Igbo a jihar Ogun
  • Mutumin da ya fusata ya koma gidan man yana mai cewa sun lalata masa injin motarsa kuma yana son ganin manajansu
  • ‘Yan Najeriya da dama da suka mayar da martani game da faifan bidiyonsa da aka yada sun ce da gaske mutane sun zama yadda suka zama a wannan zamani

Ijebu Igbo, jihar Ogun - Wani mutum a Ijebu Igbo ya fusata sosai bayan da yace an sayar masa da ruwa a madadin man fetur. Mutumin ya fuskanci gidan man don nuna fushinsa.

A cikin wani faifan bidiyo da @Instablog9ja ya yada, an nadi bidiyon mutumin tare da wani makanike yayin da mai gyaran ke taimaka masa wajen fitar da ruwan daga injin motarsa.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Bidiyon yadda aka raba danyen timatir da attarugu a wajen wani biki

Man fetur a madadin ruwa a gidan mai
Algus: Yadda aka sayar wa mai mota ruwa a madadin man fetur a wani gidan mai | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ina manajanku yake?

Ya yi korafin cewa wannan danyen aikin ya lalata injin motarsa. Wani bidiyon kuma ya nuna shi lokacin da ya dura gidan man yana neman ganin manajan gidan man don su gana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya zuba kadan daga ruwan da aka zuba masa a tankin motarsa cikin kwalabe biyu domin nuna musu abin da suka sayar masa cikin rashin sani ko ganganci.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, bidiyon ya samu dankwale sama da 5,000 tare da daruruwan sharhi.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a kamar haka:

ceemplybecca ya ce:

"Idan ba ku da mai ku rufe gidan man mana! Wannan ba kyau ko kadan."

chanty_skitchen ya ce:

"Mu ne gwamnatin da muke da ita."

florishohabuike ya ce:

"Ko'ina haka ne, kawai a kula da inda za ku sayi man fetur."

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

thebennyboom ya ce:

"Ina shawartar duk masu mota da su sami rasit ta hanyar biyan kudi ta hanyar POS a kowane gidan mai saboda za ku bukace shi a kotu, wannan shirmen ya kamata ya tsaya!"

rhx_xx7 ya ce:

"A waje daya nake siyan man fetur yanzu. Kuskure kadan; za ku ji labari."

FG ta tabbatar da cewa an samu matsala, an sayarwa gidajen mai gurbataccen fetur

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta bakin hukumar lura man feturin saman kasa NMDPR ta tabbatar da cewa an samu matsala wajen sarrafa man feturin da aka sayarwa gidajen mai.

Hukumar NMDPR ta bayyana hakan ranar Talata inda tace adadi sinadarin 'Methanol' dake cikin feturin ya yi yawa.

A jawabin da ta saki, ta bayyana cewa an gano dan kasuwan man da yake raba wannan mai kuma za'a hukuntasa yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel