Sabon salo: Bidiyon yadda aka raba danyen timatir da attarugu a wajen wani biki

Sabon salo: Bidiyon yadda aka raba danyen timatir da attarugu a wajen wani biki

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo inda aka rabawa baki danyen timatir da attarugu a matsayin kayan rabo a jihar Lagas
  • Wani daga cikin bakin da suka halarci bikin ya ce za a kara garin kwaki a kayan rabon domin ya kara armashi yayin da yake nuna nasa rabon
  • Yan Najeriya da dama sun yi martani ga bidiyon cike da barkwanci, inda suka ce wanda ya shirya taron ya yi tunani mai kyau na kayan rabo

Wani shahararren bidiyo da shafin @Instablog9ja ya wallafa a Instagram ya nuna yadda aka yi rabon danyen timatir da attarugu a wajen wani kasaitaccen biki a jihar Lagas.

Wani mutumi da ya dauki bidiyon kayan rabon da aka basa a wajen taron ya bayyana cewa wannan shine bikin da ya fi birge shi a wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Bidiyon yadda aka raba danyen timatir da attarugu a wajen wani biki
Bidiyon yadda aka raba danyen timatir da attarugu a wajen wani biki Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

An nade attarugu da timarin a leda

Mutumin ya kara da cewar za a biyo rabon da garin kwaki. Daga ganin taron ka san kasaitaccen biki ne duba ga yadda aka kawata wajen da lamomi na alfarma.

A kan teburin kowani bako da ya halarci taron, an ajiye jakar leda da ke kunshe da attarugu da tumatir.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Wannan kaya da aka raba a wajen taron ya sa mutane da yawa sun cika da al'ajabi, inda wasu suka ce wanda ya shirya taron ya yi tunani mai kyau.

iamjesspink ya yi martani:

"Kawai ina tunanin wa zai raba man fetur, wannan nake so."

liz_world25_ ya rubuta

"Wannan kayan rabo ya ba da ma'ana."

henry___efe ya ce:

"Ku da kuke dariya a shashin sharhi, kun dade baku ziyarci kasuwa bakamata yayi ku jinjinawa wadanda suka shirya taron."

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

theunbearded ta ce:

"Timatir da attarugun N5000 kenan kuke a gani a wannan jakar."

Cikin sauki: Yadda wani mutum ya yi biki mai kayatarwa, ya kashe N20,500 kacal

A wani labarin, wani sabon ango mai suna Ani Nnamdi Chris ya bayyana yadda ya angwance da amaryarsa a wani biki na sirri.

Chris ya wallafa hotunan bikin wanda ya gudana a ranar 4 ga watan Fabrairu a shafin Twitter sannan ya bayyana cewa gaba daya abun da ya kashe N20,500 ne – ya biya N15,500 na al’ada da kuma N5,000 na lemu.

A cewar Chris, bayan auren kotun, sai aka yi yar kwarya-kwaryar liyafa inda aka gayyaci mutane 10 kacal ciki harda shi da matarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel