Da Dumi-Dumi: Hukumar jin dadin yan sanda ta faɗi matakin da ta ɗauka kan Abba Kyari

Da Dumi-Dumi: Hukumar jin dadin yan sanda ta faɗi matakin da ta ɗauka kan Abba Kyari

  • Hukumar jin dadin yan sanda PSC ta bayyana cewa a halin yanzun ta jinkirta ɗaukar mataki kan Abba Kyari sabida wasu dalilai
  • Hukumar ta sanar da cewa zata jira har sai an kammala bincike, kuma ta baiwa yan sanda wa'adin mako biyu su kawo rahoto
  • Abba Kyari, wanda hukumar ta dakatar, ya shiga halin tuhuma ne bisa alaƙa da ɗan damfara Hushpuppi

Abuja - Hukumar jin daɗin yan sanda ta ƙasa ta bayyana cewa ta jingine Case ɗin da ya shafi mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari, saboda wasu dalilai.

Hukumar ta faɗi haka ne ta bakin shugaban ta, Musiliu Smith, a wurin taronta karo na 14 wanda ya gudana a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Mista Smith ya yi bayanin cewa hukumar ba zata ɗauki wani mataki kan Kyari ba a halin yanzun, har sai an kammala binciken da ta bada umarnin a sake yi.

Kara karanta wannan

Sokoto: Iyalan Ma'aikacin gwamnati da aka gano da hannu a ayyukan ta'addanci sun yi magana

Abba Kyari
Da Dumi-Dumi: Hukumar jin dadin yan sanda ta faɗi matakin da ta ɗauka kan Abba Kyari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hukumar ta dakatar da Abba Kyari ne bisa zargin alaƙa da mashahurin ɗan damfaran nan, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin dakatarwan da aka masa, Abba Kyari, shi ke jagorantar rundunar yan sandan fasaha IRT na Sufetan yan sanda na ƙasa.

Tun da farko dai, Gwarzon ɗan sandan ya fito a cikin rahoton sashin binciki FBI na ƙasar Amurka, kuma kwamiti na musamman da rundunar yan sanda ta kafa ya binciki Kyari kan zargin da ake masa.

Wa'adin mako biyu

Hukumar ta kuma bai wa yan sanda wa'adin mako biyu su kammala haɗa rahoto kan binciken Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishina.

A sanarwa da kakakin hukumar jin daɗin yan sanda, Ikechukwu Ani, ya fitar, ta bada umarnin kafa sabon kwamitin da zai bincike lamarin na daban, ban da na farko.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: An ji harbe-harben bindiga yayin da rikici ya ɓarke tsakanin mambobin NURTW

Jaridar Punch ta tattaro cewa an miƙa rahoton binciken kwamitin farko da IGP Usman Alƙali Baba, ya kafa ga ofishin Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, domin shawarwari.

A wani labarin na daban kuma Dirama ta ɓarke a Kotu yayin da Matar Aure ta yi ikirarin mijinta ya danna mata saki uku a wayar salula

Wata Kotu dake zaune a Jos ta rushe auren Ibrahim Ya'u da Amaryarsa Halima Abubakar bayan matar tace mijin ya sake ta ta Waya.

Alkalin Kotun ya karbi shawarar wakilan Mata da Mijinta, inda ya raba auren tare da umarnin Amarya ta biya Angonta sadakin da ya biya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel