Yan bindiga sun hallaka mutum 10, sun sace Hakimi a jihar Katsina

Yan bindiga sun hallaka mutum 10, sun sace Hakimi a jihar Katsina

  • Yan bindiga sun kuma kai hare-hare jihar Katsina inda suka hallaka akalla mutane goma kuma sukayi awon gaba da Hakimi
  • Wannan ya biyo bayan kisan wani Hakimi da yan bindigan sukayi a karamar hukumar Jibia makon jiya
  • Har yanzu ba'a san halin da Hakimin yake ciki ba tun bayan tafiya da shi

Katsina - Akalla mutum 13 sun rigamu gidan gaskiya yayinda akayi awon gaba da dimbin wasu a mumunan harin da yan ta'adda suka kai jihar Katsina a daren Litinin da safiyar Talata.

Premium Times ta ruwaito cewa yan bindiga sun yi dirar mikiya ne a karamar hukumar Bakori da Funtua dake kudancin jihar Katsina.

Garuruwan da aka kaiwa hari sun hada da Guga, Gidan Kanawa da Dukawa.

An sace Hakimi a jihar Katsina
Yan bindiga sun hallaka mutum 13, sun sace Hakimi a jihar Katsina Hoto: Katsina
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An sace suriki da 'yan uwan miji yayin taron sulhunta mata da miji

A hirar da manema labarai, Nafiu Muhammadu ya bayyana cewa yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin Guga, Alhaji Umar, yayinda suka hallaka mutum 10.

Yace:

"Suna zuwa suka fara harbi suna kona shagunan mutanen garin. Yayinda mutan suka fara gudu, yan bindigan suka fara harbi, hakan yayi sanadiyar mutuwar mutum 10 da na fada."
"Hakimin garin ya ki guduwa duk da cewa gidansa na nisa lokacin da aka kai harin, fuskantar yan bindigan yayi yana cewa mutanen su gudu. Lokacin suka kamashi."
"Sun kai shi gidansa inda suka kwashe kudi da kayan hatsi."

Nafiu yace Sarkin kadai aka sace kuma har yanzu ba'a birne wadanda suka mutu ba.

Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Haka a ranar Alhamis, 3 ga watan Febrairu, 2022 yan bindiga masu garkuwa da mutane suka dira garin Yangayya dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina cikin dare.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Premium Times ta ruwaito cewa yan bindiga sun kashe Dagacin garin tare da mutum hudu.

Wani mazaunin Jibia, Halilu Kabir, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun kwashe sa'o'i uku suna cin karensu ba babbaka.

Yace sun shigo kan babura kuma suka fara harbi. Yayinda suke bi gida-gida suka kashe mutum hudu da suke kokarin guduwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel