Innalillahi: Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari, sun kashe fitattun Shugabanni 7

Innalillahi: Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari, sun kashe fitattun Shugabanni 7

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun sake kai mummunan hari wata karamar hukuma a jihar Imo, sun kashe shugabanni bakwai
  • Wani haifaffen yankin da lamarin ya auku yace abun ya yi muni, maharan sun kutsa gidajen shugabanni sun kashe su
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar yace nan ba da jimawa ba hukumarsu zata fitar da cikakken bayani kan lamarin

Imo - Aƙalla shugabannin al'umma bakwai yan bindiga suka kashe a yankin Mmahu dake ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema, jihar Imo.

The Cable ta rahoto cewa yan bindiga sun halaka sanannun shugabannin mutane ne yayin da suka farmaki ƙauyen da safiyar Talata.

Shugaban al'ummar yankin baki ɗaya, Gharles Mgaraho, tare da wasu shugabanni shida na daga cikin waɗan da maharan suka kashe.

Kara karanta wannan

Karin Labari: Bayan dogon lokaci, Allah ya kuɓutar da dan uwan Jonathan daga hannun yan bindiga

Yan bindiga
Innalillahi: Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari, sun kashe fitattun shugabanni 7 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sauran waɗan da aka kashe sun haɗa da, Edeme Okoro, Issac Ojenna, Anene Funky, Chasity Paulinus, Ndubuisi Nwabuishi, da Ifeyirinwoke Junior.

Wani haifaffen ƙauyen, Elvis Iheanacho, wanda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai, ya koka kan yawan zubar da jini.

Ya kuma roƙi Allah ya, "kawo mana ɗauki kuma ya magance duk wani sheɗanin mutum ko wani mai nufin sharri ga yankin."

Yadda suka kashe manyan shugabannin

Wata majiya ta shaida mana cewa yan ta'addan sun kutsa gidajen mutanen kuma suka kashe su ɗaya bayan ɗaya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Haka nan kuma majiyar ta tabbatar da cewa yan bindigan sun tsere daga yankin bayan kammala kashe shugabannnin al'umman da suke hari.

"Har yanzun muna cikin tashin hankali, mun kasa fahimtar ainihin abin da ya faru. Yan bindigan sun shigo kauyen mu, kuma suka kutsa gidajen fitattun shugabannin mu, suka kashe su, har da babban shugaba."

Kara karanta wannan

Nasara: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannu yayin da suka kai hari Ofishin yan sandan Kogi

"Kamar mun afka yaƙi jiya. Sun buɗe wuta ba ƙaƙƙautawa har suka kashe abin harin su mutum bakwai, daga bisani suka tsere. Mun kai wa yan sanda rahoto. kuma an ɗauke gawarwakin su."

Wane matakin yan sanda suka dauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, Micheal Abbatam, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace hukumar yan sanda zata fitar da bayani ba da jimawa ba.

A wani labarin kuma Gwamnatin kasa ta haramtawa ma'aikata rungumar juna, Sunbata da kalaman batsa a wurin aiki

Kasar Mexico ta hana ma'aikatan dake karkashinta aikata wani abu da ya shafi Jima'i kamar rungumar juna da sumbatar juna a wurin aiki.

Wannan na kunshe ne a wasu sabbin dokokin da gwamnati ta fitar a hukumance ranar Talata, 8 ga watan Fabarairu 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel