An rufe makarantu a Indiya sakamakon rikicin hana dalibai sanya Hijabi

An rufe makarantu a Indiya sakamakon rikicin hana dalibai sanya Hijabi

  • An kulle Makarantun Sakandare a wani yankin kasar Indiya biyo bayan zanga-zanga kan hana dalibai sanya Hijabi
  • Wasu makarantu a watan Junairu sun hana dalibai Musulmai zana jarabawa don sun sanya Hijabi
  • Irin wannan ya faruwa a jihar Kwara, nan Najeriya ranar Alhamis inda akayi rashin rai guda kuma da dama suka jikkata

Indiya - Hukumomi a kudancin Indiya sun bada umurnin rufe makarantu ranar Talata yayinda zanga-zanga ya barke kan hana dalibai mata Musulmai shiga aji da Hijabi.

Rikicin wanda ya barke a jihar Karnataka ya tada hankulan jama'a saboda cin zarafin da yan addinin Hindu ke yiwa Musulmai karkashin mulkin Firai Minista Narenda Modi.

Zanga-zangan ranar Talata ya yi munin da sai da jami'an tsaro suka tarwatsa mutane da hayakin yaji.

Ministan yankin Basavaraj Bommai ya yi kira ga jama'a su yi hakuri da juna.

Kara karanta wannan

Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

Hakazalika ya sanar da rufe dukkan makarantun sakandaren jihar na tsawon kwanaki uku.

Yace:

"Ina kira ga dukkan dalibai, malamai da shugabannin makarantu su kasance cikin zaman lafiya da hadin kai."

An rufe makarantu a Indiya sakamakon rikicin hana dalibai sanya Hijabi
An rufe makarantu a Indiya sakamakon rikicin hana dalibai sanya Hijabi
Asali: Facebook

Me ya haddasa zanga-zanga

A watan Junairu, wasu dalibai mata a makarantar gwamnati sun bayyana cewa an hanasu shiga aji zana jarabawa saboda sun sanya Hijabi.

Wannan abu ya yadu zuwa wasu makarantun inda aka fara samun fito-na-fito tsakanin dalibai Musulmai da na mabiya addinin Hindu.

Wata dalibar da ta fuskanci wannan tsangwama a makarantar Mahatma Gandhi Memorial College, Ayesha ta bayyanawa AFP cewa:

"Ana zaune kalai suka fara cewa bai kamata muna sanya Hijabi ba... Me zasa su fara yanzu?

Ayesha tace Malaminta ya hanata zana jarabawar Kemistiri saboda ta sanya Hijabi.

Kara karanta wannan

Rikici kan sanya Hijabi a Kwara: MURIC ta fusata, ta zargi 'yan sanda da sanya wajen bincike

Mutum 1 ya mutu, da dama sun jikkata yayinda aka kaiwa Musulmai masu zanga-zanga kan hijabi hari

An nan gida Najeriya, mutum daya ya mutu, da dama sun jikkata yayinda aka farmaki iyaye masu zanga-zanga kan hana 'yayansu mata sanya Hijabi a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo, karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara.

Iyayen sun fito zanga-zanga ne saboda korar 'yayansu daga makarantar.

Wannan abu ya faru ranar Alhamis, 3 ga watan Febrairu, 2022, rahoton TheNation.

Zanga-zangar ta rikide ta koma rikici ne yayinda wasu da ake zargin Kiristoci ne suka fara jifan iyayen dake zanga-zanga a waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel