Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

  • An bankado yadda manyan hafsosin Soji suka wawure kudin makaman da gwamnatin tarayya ta basu
  • Hafsoshin Sojin mutum uku kadai sukayi babakere da kudi kimanin bilyan goma sha hudu lokacin suna sabis
  • Daya daga cikinsu yayi kokarin fita kasar waje amma jami'an hukumar Immigration sun tsareshi, sun hanashi fita

Abuja - Gwamnatin tarayya ta hana tsohon shugaban hafsan Sojin kasa, Laftanan Janar Kenneth Miniman (mai ritaya) fita daga Najeriya bisa zargin hannu cikin satar kudin makamai N13.8bn.

Hukumar shiga da fice NIS ta bayyana hakan a martanin da ta mayar wa kotu bisa shigar da ita kara da Minimah yayi a Abuja, rahoton TheNation.

Janar Minimah ya shigar da gwamnati kara babbar kotun tarayya dake Abuja bisa hanashi fita da jami'in hukumar NIS, Abdullahi Umar, da kuma kwace masa Fasfot.

Kara karanta wannan

Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida

Yace jami'in ya ci mutuncinsa kuma yayi masa barazana don kawai ya fita kasar waje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Janar Minimah
Almundahanar kudin makamai N3.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Amma a martanin hukumar NIS, Umar ya ce ya dakatad da Janar din ne bisa umurnin Gwamnatin tarayya ta ofishin hukumar hana almundahana da yaki da rashawa, EFCC.

Hukumar shiga da fice ta bayyanawa kotu cewa:

"Ba'a yiwa mutumin barazana ko wulakanci ba a tashar jirgin Nnamdi Azikwe ba kamar yadda yake ikirari."
"Bil hakki aka kwace fasfot din mutumin. Ba take hakkinsa na bil adama."
"EFCC sau biyu ta bukaci mu sanya masa ido."

Alkali Inyang Ekwo ya dage zaman zuwa ranar 1 ga Maris.

Rahoton binciken da akayi kansa

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta samu rahoto daga kwamitin binciken kudin makamai daga 2007 zuwa 2015, karkashin jagorancin tsohon Soja, Jon Ode.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Rahoton yace tsakanin 2010 da 2015 hukumar ta karbi makudan kudade amma wasu suka zuba kudaden aljihunsu.

Rahoton yace:

"Biliyoyin Naira da hukumar Soji ta samu daga wajen Gwamnatin tarayya don sayen makami amma an gano wasu manyan Soji suka wawure kudin."
"Mutanen da suka wawure Bilyan goma sha uku (N13,798,619,309) sune tsohon shugaban hafsan Soji, Laftanal Janar Kenneth Miniman; shugaban kasafin kudin hukumar Soji, Manjo Janar A. O Adetayo da tsohon diraktan kudi na hukumar, Birgediya Janar R. I Odi."

Ya akayi da kudaden

Rahoton ya cigaba da cewa:

"An tura wadannan kudaden daga baitul malin Soji zuwa asusun bankunan kamfanonin wadannan mutane da basu da wata alaka ta kasuwanci da hukumar Soji."
"Hukumar Soji da Gwamnatin tarayya sun yi asara matuka sakamakon riban da wadannan hafsoshin sukayi da kudaden nan don amfanin kansu."

EFCC tace sakamakon wannan bincike, ta rubuta wasika ga hukumar Soji ta mika mata wadannan Sojoji uku don a gurfanar da su, kuma ya kamata ace an yi tun Satumban 2020.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel