Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2

Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2

  • Gwamnati ta saka dokar ta baci na tsawon sa'a 24 a wasu kananan hukumomin jihar Niger saboda hare-haren da 'yan bindiga su ke kaiwa yankunan
  • Akwai tabbacin gwamnatin ta samu rahotanin sirri kan cewa, 'yan bindigan masu dumbin yawa za su kai farmaki cikin jihar
  • Hakan zai bada damar zakulo 'yan ta'addan da suke shirin kai har yankin, a cewar kwamishanan kula da al'amuran masarautu da tsaron cikin gida

Niger - Gwamnatin jihar Niger ta sa dokar ta baci na tsawon awa 24 a Shiroro da karamar hukumar Rafi saboda yawan hare-haren da 'yan bindiga suke kai wa yankunan.

Matakin da aka dauka sun biyo bayan rahotanin sirri da aka samu na cewa 'yan bindigan masu dumbin yawa za su kai farmaki cikin jihar, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2
Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Am sami labarin yadda aka umarci mazauna Rafi da Shiroro da su zauna a gidajen su daga karfe 5:00 na yammacin Asabar har sai baba ta gani.

An hana jama'a mazaunan kauyukan Kuta, Gwada da Zumba fita, inda aka hada su da sojoji masu tarin yawa da ke tsaron su.

The Nation ta ruwaito cewa, shugaban karamar hukumar Shiroro, Alhaji Suleiman Dauda Chukuba ne ya tabbatar da hakan. Ya ce za'a dauki duk wanda aka gani a waje a matsayin dan ta'adda.

Kwamishanan tsaron cikin gida da al'amuran masarautu na jihar, Emmanuel Umar Bagna ya roki mazauna yankunan da su bada hadin kai ga jami'an tsaron don tabbatar da zaman lafiya.

Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda

Kara karanta wannan

Za ku fuskanci zaman lafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas

A wani labari na daban, mutane da dama sun halaka sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Yayin tattaunawa da The Cable dangane da mummunan harin, Jibrin Alawa, shugaban kungiyar matasa ta jihar, ya ce harin ya auku ne da misalin karfe 3 na rana har zuwa 6 na yammacin ranar Asabar.

Alawa ya ce kusan mahara 200 ne suka afka har kauyen a baburan su rike da miyagun makamai suna harbi ko ta ina.

A cewarsa, maharan sun banka wa gidaje da dama wuta sannan sun kone sansanin ‘Yan Sa Kai da ke kauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel