Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum ya sanar da cewa da yawan tubabbun 'yan Boko Haram tuban gaskiya suka yi
  • A cewar Zulum, su ne ke taimakawa wurin yaki da ta'addanci tare da kira ga sauran abokansu da su ajiye makamansu
  • Wannan ra'ayin na Zulum ya ci karo da na takwaransa gwamnan jihar Kaduna wanda ya ce babu wata tubar gaskiya da suke yi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce kashi casa'in cikin dari na tubabbun yan Boko Haram da gaske sun ajiye makaman su sun bar ta'addanci, The Cable ta ruwaito.

Zulum ya bayyana hakan ne a wata tattauna wa da manema labaran gidan gwannati a ranar Laraba jim kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin dawo da 'yan gudun hijira gidajen su a arewa maso gabashiin Najeriya, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Za ku fuskanci zaman lafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas

Tubabbun 'yan bindiga na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum
Tubabbun 'yan bindiga na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ra'ayin sa ya sha bambam da na takwaransa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya ce babu wani abu mai kama da tubabbun yan ta'adda, Punch ta ruwaito.

Zulum ya ce, "Na yi imani sama da kashi 90 cikin 100 daga cikin tubabbun 'yan bindiga su na cigaba da gudanar da rayuwar su sannan sun bai wa gwamnati hadin kan da ya dace.
"Kuma su na kiran abokan su da ke daji da su fito su sa hannu don samar da zaman lafiya."
Yayin kaddamar da kwamitin, ya ce "Tabbas, mu na matukar farinciki, musamman wadanda cikin mu suke arewa maso gabas, saboda dubbannin mutane sun watse, wasu su na neman mafaka a jamhuriyar Chadi, jamhuriyar Niger da Kamaru.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

"Amma a wannan lokacin da gwamnatin tarayyan Najeriya, tare da gwamnatin jihohi arewa maso gabas, za ta maida hankali don ganin ta maido da 'yan gudun hijarar da su ke zaune a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
"Haka zalika, kwamitin za ta kula da tubabbun 'yan Boko Haram, kuma dukkan gwamnatocin jihohin arewa maso gabas za su ba wa kwamitin hadin kan da ya dace.
"Za mu bada hadin kan da ya dace ga gwamnatin tarayyan karkashin mulkin shugaban kasa; za mu tabbatar da goyon baya ga ministan kula da walwalar Dan Adam, sannan ma'aikatar za ta tabbatar da wannan hanyar ya haifar da da mai ido."
Ya yi tambaya idan 'yan gudun hijiran sun shirya dawowa, Zulum ya ce, "a shirye su ke. Sun matsu da su dawo tun shekara biyu da rabi da suka wuce. Amma sai dai, ba a samar musu wajen da ya dace ba.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

"Amma yanzu da gwamnatin tarayya ta zaburo, duk abubuwan da suka dace don tabbatar da dawowan su cikin mutunci gwamnati za ta tanadar musu, inda za mu yi farin ciki matuka."

Za ku fuskanci zaman kafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mazauna yankin arewa maso gabas nan babu dadewa za su fuskanci zaman lafiya da daidaito.

Buhari ya bayar da wannan tabbacin a ranar Laraba yayin kaddamar da kwamitin dawowa da 'yan gudun hijira gida a yankin, The Cable ta ruwaito.

An kaddamar da kwamitin ne bayan kammala taron maajalisar zartarwa ta tarayya, The Cable ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel