Za ku fuskanci zaman lafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas

Za ku fuskanci zaman lafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin dawo da zaman lafiya da daidaito a yankin arewa maso gabas na kasar nan
  • Buhari ya tabbatar da hakan ne yayin kaddamar da kwamitin dawowa da 'yan gudun hijira gidajensu
  • Shugaban kasan ya ce bai manta da alkawarin da yayi musu ba, kuma ba zai manta da goyon baya da karfafa guiwar da suka bashi ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mazauna yankin arewa maso gabas nan babu dadewa za su fuskanci zaman lafiya da daidaito.

Buhari ya bayar da wannan tabbacin a ranar Laraba yayin kaddamar da kwamitin dawowa da 'yan gudun hijira gida a yankin, The Cable ta ruwaito.

Za ku fuskanci zaman kafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas
Za ku fuskanci zaman kafiya nan da watanni kadan, Buhari ga 'yan arewa maso gabas. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An kaddamar da kwamitin ne bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya, The Cable ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

Tun daga shekarar 2009, yankin arewa maso gabas ta na fuskantar hauhawa na kashe-kashe, garkuwa da mutane da barnatar da kadarori wanda 'yan Boko Haram su ke yi, yanzu kuma ISWAP suka karba ragamar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A 2021, the United Nations Development Programme (UNDP), a rahoton ta na 2020 ta ce mutum 34,457 'yan ta'adda suka kashe a jihohin Borno, Adamawa da Yobe tsakanin 2009 da farkon 2020.

A yayin jawabi lokacin kaddamarwan, shugaban kasan ya ce mulkinsa ya mayar da hankali wurin dawo da zaman lafiya da daidaito a yankin.

"A farkon mulkin nan a 2015, na sha wa 'yan Najeriya alwashin cewa zan dawo da zaman lafiya yankin arewa maso gabas kuma zan dawo da yankin tafarkin cigaba. Har a halin yanzu ina nan kan baka na," yace.
"Ga jama'ar yankin arewa maso gabas, ballantana kananan yara da makomar arewa maso gabas, ba zan taba mantawa da ku ba tare da kwarin guiwa, sadaukarwa da hakurin da kuka yi da ni ba.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

"Na sha alwashin cewa nan da watanni kadan za ku fara fuskantar sauyi daga rashin tsaro zuwa zaman lafiya, daidaito da kuma cigaba a yankunan ku," yace.

Buhari Ya Isa Borno, Ya Bukaci Sojoji Su Kara Daura Damara

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya umarci sojoji da su kara himma a yaki da rashin tsaro "saboda akwai aiki da yawa da za a yi."

Daily Trust ta ruwaito. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga sojojin rundunar hadin gwiwa a filin Maimalari Cantonment a cikin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Buhari ya isa filin faretin Maimalari daidai karfe 11:30 na safe kuma ya samu tarba daga gamayyar sojoji da ‘yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel