Buhari ba zai taɓa abota da masu satar dukiyar talakawa ba, Femi Adesina

Buhari ba zai taɓa abota da masu satar dukiyar talakawa ba, Femi Adesina

  • Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce shugaban kasa ba zai taba iya abota da barayin gwamnati ba
  • A wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na Facebook ranar Alhamis wanda ya yi wa take ‘PMB da NDDC ‘, Adesina ya ce shugaban kasa ya tsani rashawa
  • Kakakin ya ce rashawar da ke hukumar ci gaban yankin Neja Delta, NDDC ya sanya shugaban kasa ya dakatar da ayyuka domin a yi kididdiga dangane da kashe-kashen kudade

Mr Femi Adesina, kakakin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shugaban kasa ba zai taba abota da masu satar kudaden gwamnati ba.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook wanda ya yi wa take, ‘PMB da NDDC’, Adesina ya ce shugaban kasa ya tsani rashawa a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari

Buhari ba zai taɓa abota da masu satar dukiyar talakawa ba, Femi Adesina
Femi Adesina: Buhari ba zai taɓa abota da masu wawushe dukiyar talakawa ba. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin ya ce tsabar rashawar da ke hukumar ci gaban yankin Neja Delta, NDDC ya sa shugaban kasa ya dakatar da duk wasu ayyuka don a yi kididdiga akan kashe-kashen kudade.

An kafa hukumar NDDC don taimaka wa mutane amma wasu sai tatsar kudi suke yi

Ya ce bisa ruwayar The Cable, an kafa NDDC ne musamman don tallafa wa mutanen yankin amma wasu mutane kalilan sun mayar da hukumar shanuwar tatsar su.

Kamar yadda ya wallafa:

“Ya kamata ta zama hukumar tallafi amma a bayyane yake, duk da dumbin biliyoyin da ake kankara wa hukumar tsawon shekaru fiye da 20, kawai wasu mutane suna kalmashe kudaden ne a asusun su maimakon yin ayyukan da suka dace.
“Akwai wani abu dangane da shugaba Buhari da ya fi tsana. Ya tsani ganin mutane masu satar dukiyoyin al’umma, ba zai taba abota da barawo ba ko wanene shi.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

“Ya dakatar da barnar da ta dade tana wanzuwa a NDDC tsawon shekaru. Don haka wajibi ne a yi kwalema mai kyau a hukumar.”

A cewarsa a yankin Neja Delta ne zaka ga takardu da yawa wadanda aka fitar da kudi ba tare da yin wasu ayyukan kirki ba.

Adesina ya yi fatan duk wanda zai gaji Buhari ya daura a tafarkin shugaban kasar

Hakan yasa a cewarsa ya kamata a gano duk masu sata ta hanyar yin kididdigar da ta dace kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Bubari ya yi.

Tun bayan Buhari ya sanya baki, kakakin ya ce NDDC ta samu ci gaba masu yawa fiye da yadda ta yi a shekaru 15 da suka gabata.

Ya ce hakan abu ne da mutane da dama suke ganin da kyar ya yuwu amma sai ga shi ya yuwu. Adesina ya shawarci mutane akan zabar shugaban da ya dace a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

Kamar yadda ya wallafa:

“Yayin da 2023 take karatowa, ina fatan ‘yan Najeriya zasu hada kai wurin zaben shugaba wanda zai tallafa wa kasa kamar yadda Buhari ya yi. Muna fatan ba za a bijire wa hanyoyin da ya sanya mu a kai ba, Amen.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel