Wata sabuwa: Mambobin APC sun kawo wargi, sun nemi a dage taron gangamin 26 ga wata

Wata sabuwa: Mambobin APC sun kawo wargi, sun nemi a dage taron gangamin 26 ga wata

  • An bukaci jam’iyyar APC mai mulki da ta gaggauta dage shirinta na gudanar da taron gangamin jam’iyyar na kasa da aka shirya a watan nan
  • ‘Yan jam’iyyar mazauna kasar Birtaniya ne suka yi wannan kiran a ranar Talata 1 ga watan Fabrairu
  • Mambobin jam’iyyar APC a kasar Birtaniya sun ce kamata ya yi jam’iyyar ta mayar da hankali wajen ganin an warware rikicin da ke tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a matakai daban-daban

Landan, Burtaniya - A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke shirin gudanar da taron gangaminta na kasa, reshen jam’iyyar na Burtaniya (UK) ta shawarci majalisar zartarwar jam'iyyar ta kasa da ta sake shawara.

Jam’iyyar APC reshen Burtaniya ta shawarci jam’iyyar da ta hada karfi da karfe kan cimma nasarorin da Gwamna Mai Mala Buni ke son cimmawa a kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya (CECPC).

Kara karanta wannan

2023: Mai neman kujerar shugaban kasa a PDP, ya dawo gida zai yi takarar Gwamnan Jiha

APC a Burtaniya ta caccaki Najeriya
Wata sabuwa: Mambobin APC sun kawo wargi, sun nemi a dage taron gangamin 26 ga wata | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC reshen Burtaniya, Philip Idaewor, wacce aka aikowa Legit.ng, kungiyar ta yi imanin cewa yana da kyau jam’iyyar ta samu karin dalilan sasanta ‘ya’yanta.

Idaevor ya ce ‘ya’yan jam’iyyar a kasar Birtaniya suna son hukumomin APC su sauya taron gagamin na kasa da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 26 ga watan Fabrairu zuwa wani lokaci daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce shawarar za ta tabbatar da samun halartar ‘ya’yan jam'iyyar dake kasashen waje domin ba za su iya ware kudaden jigila har sau biyu ba zuwa Najeriya don halartar taruka biyu.

Jam’iyyar APC reshen kasar Birtaniya ta yi kira ga hukumomin jam’iyyar da su yi kira ga jam’iyyar da ta dage taron domin moriyar dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Samar da jituwa tsakanin 'yan jam'iyyar APC tare da shirin zaben 2023

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta kyale ‘Dan Arewa ya sake karbar tutan takarar shugaban kasa

Ya kara da cewa, samar da hadin kai, zaman lafiya da fahimta a cikin jam’iyyar ya fi komai dacewa fiye da taron gangamin da nan da makonni uku masu zuwa zai kara dagula jam’iyyar.

Idaewor ya ce rahotanni daga gida (Najeriya) game da yadda jam’iyyar APC ke fama da 'yan tawaye da dama a yawancin jihohinta ba su da kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta samu lamuni a zabe mai zuwa na 2023.

A ci gaba da yin kira ga shugabannin jam’iyyar da su tashi tsaye wajen sasantawa, Idaevor ya ce jam’iyyar APC a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu nasarori da dama wajen gina kasar nan.

A wani labarin, saura kwanaki uku a yi taron gangamin APC, amma har yanzu jami'yyar bata sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ba game da taron da za a yi a ranar 26 ga Fabrairu, 2021 ba.

Kara karanta wannan

Yadda zan bi wajen shawo kan rigingimun jam’iyya idan na zama Shugaban APC inji Sanata

Kwamishinan wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri'u na INEC, Mista Festus Okoye, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Punch jiya Talata.

Okoye ya ce:

"Ba a sanar da hukumar ba game da wani taron gangami."

Asali: Legit.ng

Online view pixel