2023: Mai neman kujerar shugaban kasa a PDP, ya dawo gida zai yi takarar Gwamnan Jiha

2023: Mai neman kujerar shugaban kasa a PDP, ya dawo gida zai yi takarar Gwamnan Jiha

Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa da shi za a gwabza wajen neman tikitin takarar gwamna

A zaben 2023, Baba-Ahmed zai nemi kujerar Gwamna a jihar Kaduna, yana sa ran ya gaji El-Rufai

‘Dan siyasar ya nemi ya fito takarar shugaban kasa a 2019, amma bai iya samun tutar jam’iyyar adawa ba

Kaduna - Yusuf Datti Baba-Ahmed, daya daga cikin jagororin jam’iyyar hamayya a Najeriya ya nuna sha’awar tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 31 ga watan Junairu 2022, inda aka ji cewa Dr. Datti Baba-Ahmed ya bayyana muradinsa a zabe mai zuwa.

Baba-Ahmed ya bayyana neman takarar gwamnansa a matsayin kokarin yi wa al’ummarsa hidima.

A cewarsa, zai fitar da jama’a daga kangi, sannan yi kokarin samar da jihar da kowa yake sha’awa. ‘Dan siyasar ya ce ba kwadayin mulki ta sa zai yi takara ba.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

A zaben 2019, Baba Ahmed yana cikin wadanda suka nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, amma ya sha kashi a hannun Atiku Abubakar.

Gwamnan gobe
Yusuf Datti Baba-Ahmed Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jawabin Yusuf Datti Baba-Ahmed

“Mutanenmu su na matukar bukatar shugaba na gari wanda zai tsare rayukansu, da dukiyoyinsu, kuma ya kawo cigaba a jihar.”
“Ba na zo neman kujera ko mukami ba ne, amma halin wahalar da al’umma s uke ciki ya sa nake neman jagorantar ‘Yan Kaduna.”
“Shugaba na gari shi ne wanda zai iya magance matsalolin zamantakewarsu, kuma ya kawo cigaba da kwanciyar hankali.”
“Saboda haka za mu gaza idan har muka gagara zakulo shugabannin kwarai da za su inganta rayuwar al’ummarmu.”

- Yusuf Datti Baba-Ahmed, Ph.D

Jaridar Pulse ta rahoto Datti Baba Ahmed yana cewa ana bukatar gaskiya, amana da ke-ke-da-ke-ke a wajen shugaba idan dai har ana so rayuwar al’umma ta gyaru.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta kyale ‘Dan Arewa ya sake karbar tutan takarar shugaban kasa

Wa zai rike Kaduna a 2023?

Kwanakin baya mun kawo maku rahoto na musamman cewa an fara lissafin wanda jam’iyyar APC za ta tsaida takarar Gwamna a jihar Kaduna a zabe mai zuwa.

Sanata Uba Sani, Bashir Sa’idu da Muhammad Sani Abdullahi watau Dattijo su na cikin wadanda ake ganin za su gwabza a Jam’iyyar APC wajen samun tikitin takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel