Duniyar crypto: Yayin da 'yan crypto ke ta kukan faduwa, kamfanin crypto ya tara N13tr

Duniyar crypto: Yayin da 'yan crypto ke ta kukan faduwa, kamfanin crypto ya tara N13tr

  • Kamfanin nan crypto da ke Bahamas ya tara dala tiriliyan 13 na kudade kamar yadda kamfanin ya fada a ranar Litinin, 31 ga Janairu, 2022
  • FTX ya ce a baya ya samu Naira biliyan 166 a cikin wani tallafi na Series C wanda ya zama na uku na tattara kudade a cikin watanni tara da suka gabata
  • Shugaban kamfanin FTX, Sam Bankman-Fried ya ce kamfanin yana tunanin fitowa fili ga kowa da kowa amma ba nan gaba kadan ba

Wani dandalin cinikayya da musayar crypto na FTX ya shaida darajar karuwar kudade zuwa Naira tiriliyan 13.2 a wani zagaye na fannin zuba jari na 'funding' a ranar Litinin, 31 ga Janairu, 2022.

Legit.ng ta gano cewa, wannan yana nuna cewa akwai babbar ci gaba ga kasuwar crypto duk da koma bayan da aka samu a fannin sakamakon sanya daga masu saka hannun jari yayin da farashin kaya ke ci gaba da faduwa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

Matashi Sam Bankman-Fried mai kamfanin FTX
Yayin da 'yan crypto ke cikin wani hali, wani kamfanin musayar crypto ya habaka da biliyoyi | Hoto: bwbx.io
Asali: UGC

FTX ta ce ta tara Naira biliyan 166 a zagayen 'funding' na Series C wanda hakan ya sa ta tara kudade na uku a cikin watanni tara da suka gabata.

FTX na daya daga cikin manyan kafofin musayar crypto a duniya kuma tana ba da dama da hanyoyi da dama na yin musayar kudaden crypto a kan manhajar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamfanin wanda ba a san da shi ba a baya ya zama babban jigo a sabuwar kasuwar crypto, a yanzu dai yana gogayya da kamfanonin musaya irinsu Coinbase da jagoran kasuwar crypto wato Binance.

Kamfanin FTX ya tara Naira biliyan 830 a fannin 'funding' ya zuwa yanzu kuma ya tara makudan kudade a daidai lokacin da farashin kudaden crypto suka ragu matuka.

Koma bayan Bitcoin a kwanakin nan

Bitcoin ya ragu da 46% cikin 100% idan aka kwatanta da kusan Naira miliyan 29 a watan Nuwamba, kuma wasu kudade da dama na crypto ma sun durkushe.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ya samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP

Wannan ya kara tsananta fargabar cewa alamar na iya kasancewa a kan gaba ga mafi tsanani 'hunturun duniyar crypto'.

Irin wannan ya faru a baya a karshen 2017 da farkon 2018 lokacin da Bitcoin ya ragu da kusan 80% daga wancan lokacin.

Sam Bankman-Fried Shugaba kuma wanda ya kafa kafar FTX ya ce kasuwar crypto na iya shiga dogon hunturu, a cewar wani rahoton CNBC.

Ya ce sauye-sauye sun faru a cikin tsammanin farashin riba, kuma kasuwannin crypto suna motsawa a yanzu.

Ya ce kamfaninsa ya yi ta tunanin bayar da kyauta ga jama'a a karon farko amma ba shi da shirin yin hakan nan take.

A wani labarin daban, Daniel Maegaard a da yana samun Naira 6,500 kacal a kowane awa idan ya yi aiki a wani gidan mai a karshen mako yayin da yake karatun ilimin halayyar dan adam a wata Jami'ar.

Kara karanta wannan

Karon farko tun 2014: Ana cece-kuce kan cire tallafi, farashin danyen mai ya kai $90

Maegaard ya kasance yana tara kwabban crypto yayin da yake hada aikinsa da karatu amma gogewa a fannin fasaha da sa'ar rayuwa sun sa ya zama hamshakin attajirin dare daya.

Ya yi tuntube da wani tsagin duniyar crypto da ake kira Non Fungible Tokens (NFTs) shekaru kafin su zama abin da suke yanzu. Wannan ya ba shi damar zama miloniya a cikin shekaru goma da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel