Dare daya: Yadda dan crypto ya zama miloniya a wata sabuwar duniyar crypto wai ita NFT

Dare daya: Yadda dan crypto ya zama miloniya a wata sabuwar duniyar crypto wai ita NFT

  • Wani mutumin da ke aiki a matsayin ma'aikacin gidan mai a karshen makon da ya gabata ya zama hamshakin attajiri lokacin da ya gano wata harka a duniyar crypto
  • Daniel Maegaard a da yana samun N6,500 ne kadai a kowane awa lokacin da ya yanke shawarar siyan hannun jari a crypto
  • Bayan saka hannun jarin, Maegaard ya yanke shawarar mayar da jarinsa na Naira miliyan 1.6 zuwa tsarin kasuwar NFTs kuma anan ya samu sama da Naira biliyan 40.

Daniel Maegaard a da yana samun Naira 6,500 kacal a kowane awa idan ya yi aiki a wani gidan mai a karshen mako yayin da yake karatun ilimin halayyar dan adam a wata Jami'ar.

Maegaard ya kasance yana tara kwabban crypto yayin da yake hada aikinsa da karatu amma gogewa a fannin fasaha da sa'ar rayuwa sun sa ya zama hamshakin attajirin dare daya.

Kara karanta wannan

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

Miloniyan crypto da baku san dashi ba
Ma'aikacin gidan mai kudin shiga N6,500 ya zama miliyoniya ta dalilin NFT | Hoto: Dimitri Otis
Asali: Getty Images

Ya yi tuntube da wani tsagin duniyar crypto da ake kira Non Fungible Tokens (NFTs) shekaru kafin su zama abin da suke yanzu. Wannan ya ba shi damar zama miloniya a cikin shekaru goma da suka gabata.

Ciniki mai gwabi guda daya na CryptoPunk NFT a watan Mayu 2021 ya caje shi Naira miliyan 7.4 a lokacin wanda yanzu darajarsa ta haura sama da biliyan N20.7.

Farkon 'yan crypto a duniya

Wayayyen dan crypton, wanda ya yi yawon duniya zuwa kasashe sama da 50, ya ce komai ya fara ne tun lokacin da ya fara jin labarin Bitcoin a shekarar 2013, shekaru takwas da suka wuce.

Ya ce yana jinkiri a kan aikinsa. Ya ce bai taba son zama masanin ilimin halayyar dan adam ba, a cewar rahoton New Zealand Herald.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

A cewarsa, ya yi tuntube da batun ne a wani labari na BBC inda ake magana game da hauhawar farashin Bitcoin, wanda ya tashi daga N8,300 nan take zuwa sama da N20,700.

A lokacin, Maegaard yana karatun shari'a bayan ya kammala karatunsa na digiri a fannin ilimin halayyar dan adam lokacin da crypto ta fara hauhawa a 2017. Ya ce ya sami isasshen kudi a 2017 don jin dadin rayuwarsa.

Mutumin mazaunin Queensland ya saka hannun jari a cikin kasuwannin blockchain, musamman Bitcoin, PP coin, Lite Coin da Ripple XRP.

Ribarsa a hannun jarin crypto ya haura da 1000% ba wai 100% ba yayin da Ripple ya fire sama fiye da Bitcoin a waccan lokacin, wanda ya karu da 36,000% a cikin shekara guda.

Ya ce mutanen baya sun ba wa harkar crypto mummunan suna. A farkon 2017, Maegaard ya fara da saka hannun jari a crypto da kusan Naira miliyan 50. A cikin Afrilun 2017, ya zama miloniyan da bai yi zato ba.

Kara karanta wannan

A Najeriya: Yadda matashi dan shekaru 17 ya juya N1000, ya zama miloniya a wata 6

Maegaard ya ce bai taba jin dadin rayuwa ba kamar yadda a yanzu zuciyarsa ke cike da farin ciki.

Ya natsu sosai, tare da saita hangen nesa a fannin crypto kuma ya kara saka hannun jari. A karshen 2017, Naira miliyan 41.5 dinsa sun haura zuwa Naira Biliyan 8.3.

Lokaci yayi masa dariya a yanzu, in ji Maegaard.

Ya fita da fitarsa

Ya cire da Naira biliyan 4.1 daga kasuwar crypto sannan ya sanya su a wata katafariyar harkar kasuwanci sannan ya sayi makeken gida a Australiya.

A wannan lokacin, wannan dan cryoton yana da Naira miliyan 74.7 a kudadensa na shiga da bai damu dasu ba wanda ke shiga asusunsa daga masu hayan gidan da ya saya a Australiya.

Ya sayi CryptoPunk 8348, wanda yake da mahimmanci saboda karancinsa.

CryptoPunks wani damin NFT ne da ake iya sauyawa zuwa Ethereum da aka kaddamar a cikin 2017 a Larva Labs, kamar yadda DailMail ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da hatsabibin ɓarawo dauke da IPhones 16, kwamfuta da wasu kayayyaki a Oyo

Gaba daya, akwai CryptoPunk guda 10,000 ne na musamman kuma wannan zane gaba daya kebabbe ne, ma'ana babu wanda zai iya canza lambarsa, kuma hakan na nufin ba za a taba samun sama da 10,000 ba kwata-kwata.

A wani labarin na daban, a zamanin nan, wayoyin tafi da gidanka sun zo da abubuwa masu yawa ga mutane da yawa.

Wani dalibi dan kasar Indonesiya, Sultan Gustaf Al Ghozali, ya shiga wata duniyar fasahar mai sarkakiya, inda ya sayar da hotunansa na selfie a kan kudi naira miliyan 415. Hakan ya sa ya zama miloniya dare daya.

Dalibin mai shekaru 22 na Kimiyyar Kwamfuta ya canza kusan dukkanin hotunansa guda 1,000 zuwa fasahar kadarar crypto ta NFTs.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags:
Online view pixel