Karon farko tun 2014: Ana cece-kuce kan cire tallafi, farashin danyen mai ya kai $90

Karon farko tun 2014: Ana cece-kuce kan cire tallafi, farashin danyen mai ya kai $90

  • Farashin man fetur ya kai $90 a wata na takwas tun daga 2014 a ranar Laraba 26 ga watan Junairu, 2022 a daidai lokacin da rikicin kasa da kasa ke tsakanin Rasha da Ukraine
  • Matsayin Amurka ya daidaita a 2.04%, wanda ya kai $90.47 kowace ganga a karon farko cikin shekaru 8 tun daga 2014
  • Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirinta na cire tallafin man fetur biyo bayan korafe-korafen jama'a wanda ya shafi hauhawar farashin kayayyaki

Farashin danyen mai na Brent ya kai dalar Amurka 90 a ranar Laraba, 26 ga Janairu, 2022, a karon farko tun 2014 yayin da yake ci gaba da yin fintinkau, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Wannan ci gaban da aka samu ya zo ne yayin da tashin hankalin tsagi da ke tsakanin Rasha da Ukraine ke karuwa da kuma raguwar samar da kayayyaki ke ci gaba da tsananta da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince a bada kwangilolin wasu tituna 16 da za su ci Naira Biliyan 64

Farashin danyen mai ya tashi a duniya
Karon farko tun 2014: Ana cece-kuce kan cire tallafi, farashin danyen mai ya kai $90 | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Man ya karu da fiye da 2$ a lokaci guda, inda ya kai dala $90.47 a karon farko tun daga 2014. Ya ja baya a takaice da rana, inda ya kai 2% a kan $89.96 kan kowacce ganga.

Babban tashi a cikin shekaru 8

Matsayin mai na Amurka ya daidaita da 2.04% a 87.35% a kowace ganga. A lokacin, tashin ya kai %$87.05 kamar yadda aka gani na karshe a watan Oktoban 2014.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Goldman Sachs, masani a harkar, ya fada a ranar Laraba, 26 ga Janairu, 2022, cewa batun tushe na kamfanoni da ke da alaka da tashin shine cewa ba zai yiwu a samu cikas ga samar da kayayyaki ba, amma ana iya samun koma baya ga farashin makamashi da aka sanya wa farashi mai tsauri.

Barclays ya lura cewa yayin da farashin zai iya zama mai alaka da wani bangare na "diyya ta yanki," tushen ka iya haifar da habaka mafi girma.

Kara karanta wannan

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

Kungiyar OPEC da takwarorinta masu samar da man fetur suna ta mayar da danyen mai zuwa kasuwa, amma kungiyar ta kasa samar da hako mai domin kaiwa ga cimma burinta.

A halin da ake ciki, habakar mai na Amurka ya ragu, kuma annobar Korona ta Omicron bata kasance daya daga dalilan da aka fara sa rai akansu ba.

Batun cire tallafin mai a najeriya

A ranar Larabar da ta gabata ce ministar kudi ta Najeriya, Zainab Ahmed, ta ce hukumar kula da albarkatun man fetur ta Najeriya (NNPC) ta gabatar da kudirin doka na Naira tiriliyan 3 domin samar da tallafin mai a 2022.

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na cire tallafin man fetur daga watan Yuli, saboda "yawan hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin tattalin arziki" .

An yi shawarar tsawaita yiwuwar karin zuwa watanni 18 kafin a daidaita bangaren man fetur daidai da dokar masana'antar man fetur.

Kara karanta wannan

Dare daya: Yadda dan crypto ya zama miloniya a wata sabuwar duniyar crypto wai ita NFT

A halin da ake ciki, hahawar farashin danyen man fetur a duniya ya sanya saukar farashin man fetur da ake shigo da shi Najeriya zuwa sama da N282 kan kowace lita, inji rahoton Punch.

Karin hauhawar farashin man fetur din na nufin karin tallafi saboda farashin man fetur ya tsaya a lokaci mai tsawo akan N162-N165 kowace lita.

A baya kunji cewa, jaridar TheCable ta rahoto cewa, farashin danyen mai na Brent, ya tashi zuwa $88 a kowacce ganga a ranar Talata, bisa tsauraran matakan da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC da kawayenta ke samarwa.

A ranar Talata, makomar danyen mai na Brent ya samu 1.65% zuwa $88.11 kan kowace ganga daya a karfe 8:41 GMT+1, yayin da US West Texas Intermediate ya karu da 20.8% zuwa $85.73, 0.54% na ICE na London da ya kai $87, in ji rahoton APA.

Morgan Stanley, wani bankin zuba jari na kasa da kasa, ya yi hasashen cewa danyen mai na Brent zai iya haura $90 a cikin kwata na uku na wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Hadarin mota a Kano: Mutum 9 sun mutu, 10 sun jikkata yayin da wata mota ta kubce

Asali: Legit.ng

Online view pixel