Allahu Akbar: Babban wasiyyar da mahaifina Sheikh Albany Zaria ya bari kafin ya cika, Abdurrahman

Allahu Akbar: Babban wasiyyar da mahaifina Sheikh Albany Zaria ya bari kafin ya cika, Abdurrahman

  • Yayin da Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albany Zaria ke cika sheƙara 7 da rasuwa, an yi fira da babban ɗansa, Abdulrahman
  • Abdulrahman Muhammad Auwal, ya bayyana wata wasiyya da Mahaifinsa ya bar musu, wacce ba za su manta da kalaman malamin ba
  • A shekarar 2014, wasu mahara suka tare babban Malamin a kan hanyarsa ta komawa gida, suka harbe shi da iyalansa

Zaria, jihar Kaduna - Babban ɗan shahararren malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Muhammad Auwal, wanɗa aka fi sani da Albany Zaria, ya ce mahaifinsu ya bar wasiyyar da ba zasu taɓa mance wa da ita ba.

A wata fira da sashin Hausa na BBC, ya ce babbar wasiyyar da mahaifinsu ya bar musu kafin rasuwarsa shi ne su maida hankali kan neman ilimi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ni da Masari ba mu bacci idanu 2 rufe, Sarkin Katsina ga Osinbajo

Ɗan marigayin, Abdulrahmad Muhammad Auwal, ya ce bayan rasuwar mahaifin su, rayuwar iyalansu ta shiga kalubale babba ta wannan giɓin rashin sa a cikin su.

Marigayi Sheikh Albany
Allahu Akbar: Babban wasiyyar da mahaifina Sheikh Albany Zaria ya bari kafin ya cika, Abdurrahman Hoto: theabusites.com
Asali: UGC

Abdulrahman, wanda aka fi sani da Abu Huraira ya ce:

"Abubuwan da na fi tunawa a raina (game da shi) su ne kiran da yake nanata mana mu maida hankali wajen karatu. Na kan yawan tuna waɗan nan kalmomin musamman da yake cewa ba mu da gatan da ya wuce karatu."
"Alhamdulillah muna kara gode wa Allah domin karatu kam muna kan yi, kuma muna yi iya bakin gwargwadon hali."

Abu Huraira ya ƙara da cewa abin da yake wa iyalan Malam daɗi shi ne yadda ɗalibansa da ya gina suka ɗora daga inda ya tsaya, abubuwan alheri na ilimi da ya bari suna cigaba ta hannun su.

Kara karanta wannan

Jigon Arewa: Laifin 'yan Arewa ne suka sa Jonathan ya gaza karar da Boko Haram

Yaushe ne rabuwarka ta ƙarshe da Malam?

Babban ɗan marigayi Albany ya bayyana cewa firarsa ta karshe da Malam shi ne ranar da yazo masa bankwana zai koma makaranta, mako ɗaya kafin a kashe shi.

"Mako ɗaya ƙafin rasuwarsa na je na same shi, na faɗa masa zamu koma makaranta kuma ya mun addu'a. Washe gari na koma makaranta."
"Ranar Asabar kawuna ya kira ni ya sanar da ni abin da ya faru, an kashe Malam, na yi kokarin fitowa na nemi mota da tsakar daren nan na dawo gida."

Shekara Bakwai da kashe Albany

A shekarar 2014, wasu yan ta'adda suka farmaki malamin yayin da yake kan hanyar komawa gida daga makaranta a birnin Zariya.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun harbi Malamin da iyalansa, nan take matarsa ta rasu, amma Albany da ɗansa sai da aka kai su Asibiti sannan suka cika.

A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya Musulunta saboda kallon shirin IZZAR SO na masana'antar Kannywood

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje a jihar Kano ya ɓace

Wani bawan Allah ya karbi kalmar shahada ya shiga Addinin Musulunci saboda kallon shirin Izzar So da yake yi.

Lawan Ahmad wato Umar Hashim a shirin Izzar So, shine ce ya faɗi haka, kuma ya sanya bidiyon mutumin na maimata kalmar shahada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel