Jigon Arewa: Laifin 'yan Arewa ne suka sa Jonathan ya gaza karar da Boko Haram

Jigon Arewa: Laifin 'yan Arewa ne suka sa Jonathan ya gaza karar da Boko Haram

  • Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, ya magantu a kan lamarin rashin tsaro da ya addabi kasar
  • Aliyu ya yi zargin cewa wasu yan arewa ne suka sa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kasa murkushe Boko Haram saboda wasu dalilai na siyasa
  • Ya ce a wancan lokacin sun zata Jonathan ba zai mika mulki ba ko da ya sha kaye a zabe

Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya ce wasu yan arewa ne suka sa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kasa murkushe Boko Haram.

Da yake magana a yayin wata hira da jaridar Punch, tsohon gwamnan ya ce abin takaici ne yadda aka bar rashin tsaro ya ta’azzara.

Jigon Arewa: Laifin 'yan Arewa ne suka sa Jonathan ya gaza karar da Boko Haram
Jigon Arewa: Laifin 'yan Arewa ne suka sa Jonathan ya gaza karar da Boko Haram Hoto: The Cable
Asali: UGC

The Cable ta nakalto Aliyu yana cewa:

Kara karanta wannan

'Dan Sarauniya: Lauya ya bayyana dalilin da yasa ƴan sanda suka kama tsohon kwamishinan Ganduje

“Lokacin da Boko Haram ya fara sannan gwamnatin Umaru Musa Yar’Adua da Goodluck ta fara yin wani abu a kai, sai lamarin ya fada karkashin Jonathan don ya ci gaba. Yan arewa da dama suka yiwa matsayin Jonathan wani irin fahimta saboda dalilai na siyasa, suna ta korafe-korafe da ya hana aiwatar da manufofin da suka dace wanda da sun kawar da Boko Haram kuma gashi har yanzu muna fama da su.
“Fashin daji wanda da dama daga cikinmu suka zata ba zai taba faruwa ba, har yanzu ban ji daga kowa ba game da jawabin da aka alakanta da Kawu Baraje, tsohon shugabanmu na PDP na kasa a jihar Kwara, lokacin da ya bayyana cewa sun kawo yan fashin daji ko Fulani daga sauran wurare. Ina ganin bisa tunanin cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ba zai mika mulki ba koda sun yi nasara, amma sai ya mika.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

“Ya taya su murna tunma kafin a kammala kirga kuri’u wanda ya kawar da duk manufar kawo wadannan mutane kuma da zan yi tunanin cewa idan wannan gaskiya ne, toh wadanda suka kawo su za su basu toshiya domin su koma inda suka fito.”

Da yake ci gaba da magana, Aliyu ya ce ya yarda cewa:

“Idan da gwamnoni sun yi kokari daga 2015 zuwa yanzu, da mun kawar da fashi da makami.
“A yau abun takaici ne cewa sai mutum ya yi ta addu’a idan ya bar Abuja zuwa Kaduna ko Kaduna zuwa Abuja ko kuma musamman a jihohin arewa.
“Yanzu hatta da rana, ba za ka iya tuki hankali kwance ba. Don haka, na yarda cewa matakin farko na yakar rashin tsaro sune gwamnoni. Watakila kun ji ni a Kano lokacin da nake cewa shin mutum daya zai iya fin 19 saboda a lokaci daya, koda dai yanayin sun banbata, muna da mutum daya kan jihohi 19 sannan a yanzu muna da gwamnoni 19 amma duk da haka muna da matsaloli fiye da yadda muke da su a baya."

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

A wani labari na daban, Shugaban cocin superintendent of Glorious Vision World Outreach Ministries, Rev (Dr.) David Oyediran, ya yi hasashen cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci Najeriya.

A cewar faston, Tinubu na daya daga cikin yan tsirarun mutane da za su iya gyara kasar a matsayin shugaban kasa.

Oyediran a jawabinsa mai taken ‘Nufin Allah kan Najeriya’, ya ce Allah ya nuna masa hakan ne bayan yiwa kasar gagarumin addu’a, The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel