NNPC: Mun kashe biliyan N100 wajen gyara matatun mai a 2021

NNPC: Mun kashe biliyan N100 wajen gyara matatun mai a 2021

  • Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ta ce ta kashe naira biliyan 100 wajen gyara matatun mai a shekarar 2021
  • Duk da cewar ba a ambaci ainahin matatun da aka kashewa kudin ba, NNPC ta ce ta kashe naira biliyan 8.3 duk wata a shekarar 2021 don gyara matatun
  • Matatun man da ke karkashin NNPC suna a Port Harcourt, Kaduna da kuma Warri ne

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ta kashe naira biliyan 100 wajen gyara matatun man kasar a 2021.

Bayanin na kunshe ne a jawabin da NNPC din ta yi a taron kwamitin FAAC kan ayyukan da ta dauki nauyi a shekarar, The Cable ta rahoto.

A cewar kamfanin man kasar, an yi amfani da kudin ne wajen gyara matatun a tsawon shekarar.

Kara karanta wannan

An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

NNPC: Mun kashe biliyan N100 wajen gyara matatun mai a 2021
NNPC: Mun kashe biliyan N100 wajen gyara matatun mai a 2021 Hoto: guardian.ng
Asali: Facebook

Koda dai ba a ambaci ainahin matatun ba, a bisa ga rahoton kudin, NNPC ta ce ta kashe naira biliyan 8.3 duk wata a shekarar 2021 don gyara matatun, rahoton Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matatun da ke karkashin hukumar NNPC din sun hada da kamfanin tace mai na Port Harcourt (PHRC), kamfanin tace mai na Kaduna (KRPC) da kamfanin tace mai na Warri (WRPC).

Gaba daya matatun na samar da gangar mai 445,000 a kowace rana.

Duk da kasancewar tana da matatun mai hudu, Najeriya na shigo da man da aka tace mata daga waje. Sakamakon haka, kasar na kashe kudaden waje don tabbatar da ba a samu karancinsa ba.

Mele Kyari, babban daraktan NNPC, ya ce da gangan aka rufe matatun man kasar saboda ayyukansu ba za su iya ci gaba da dorewa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya na zargin NNPC da laifin sata da noke gaskiya a kan batun man fetur

A watan Maris 2021, kwamitin FEC ya amince da dala biliyan 1.5 domin gyara matatar man Port Harcourt.

A makon da ya gabata, gwamnatin tarayya ta ce ta biya dala miliyan 98 da kuma naira biliyan 17.2 a matsayin wani kaso na kudaden aikin gyaran matatar man da ke gudana.

Labari mai dadi: Matatar mai ta Dangote za ta fara aiki a kwata na uku a 2022

A wani labarin, mun ji a baya cewa Shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya ce matatar mansa za ta fara sarrafa danyen mai a kwata na uku na shekarar 2022.

A bisa rahoton Bloomberg, shahararren dan kasuwar ya ce an yi aikin injina a matatar, kuma "muna sa ran kafin karshen kwata na uku za mu kasance a kasuwa."

Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a wurin aikin gina matatar da ke gudana a Legas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata kara kudin mai bayan zaben 2023, Minista Mai

Asali: Legit.ng

Online view pixel