Labari mai dadi: Matatar mai ta Dangote za ta fara aiki a kwata na uku a 2022

Labari mai dadi: Matatar mai ta Dangote za ta fara aiki a kwata na uku a 2022

  • Rahotanni sun kawo cewa matatar mai ta Dangote za ta fara sarrafa danyen mai a kwata na uku na shekarar 2022
  • Shugaban rukunin kamfanonin kuma mai kudin Afrika, Aliko Dangote ne ya bayyana hakan
  • Ya ce matatar zata fara aiki tare da tace gangar mai 540,000 a kowace rana kafin abubuwa su kankama da kyau

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya ce matatar mansa za ta fara sarrafa danyen mai a kwata na uku na shekarar 2022.

A bisa rahoton Bloomberg, shahararren dan kasuwar ya ce an yi aikin injina a matatar, kuma "muna sa ran kafin karshen kwata na uku za mu kasance a kasuwa."

Labari mai dadi: Matatar mai ta Dangote za ta fara aiki a kwata na uku a 2022
Labari mai dadi: Matatar mai ta Dangote za ta fara aiki a kwata na uku a 2022 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a wurin aikin gina matatar da ke gudana a Legas.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023

Dangote ya ce kamfanin zai fara aiki tare da tace gangar mai 540,000 a kowace rana.

Ya ce:

"Cikakken aiki na iya farawa watakila a karshe ko farkon shekarar 2023."

Matatar man Dangote gagarumin aiki ne na biliyoyin daloli wanda zai samar da kasuwar danyen man Najeriya akan dala biliyan 11 a duk shekara.

Matatar wacce aka kashe a kalla dala biliyan 19 wajen gina ta, za ta iya tace gangar mai 650, 000 a kowace rana.

Ana sanya ran matatar man za ta zama mafi girma a Afrika kuma daya daga cikin manyan matatu masu zaman kansu na duniya, da zaran an kammala ta.

Wannan zai sa Najeriya da wasu kasashen Afrika su daina shigo da mai domin zai wadace su sosai.

Kara karanta wannan

Babbar magan: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa da zarar matatar ta fara aiki a shekarar, Najeriya za ta samu rarar kaso 40 na kudin da take samu a waje, rahoton The Cable.

Arzikin Ɗangote ya ƙaru da $1.3bn a cikin makonni 3, kwatankwacin ƙarfin tattalin arzikin Senegal

A wani labarin, mun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya samu karuwar arziki da kimanin Dala biliyan 1.3 (N539,435,000,000.00) a farkon shekara zuwa ranar 21 ga watan Janairu, a cikin wannan lokacin masu hannu jari a kamfanin simintin Dangote sun samu alheri, rahoton Premium Times.

A halin yanzu arzikin sa ya tasanma na Dala biliyan 20.4 a cewar kididigar Biloniyoyi na Bloomberg a ranar Juma'a, hakan na nufin arzikin na dan kasuwan mafi arziki a Afirka ya kai kusan karfin tatttalin arzikin kasar Senegal da Bankin Duniya ta kiyasta ka Dalla biliyan 24.9.

Dangote ya samu wannan karuwar arzikin ne bayan masu saka jari sun siya hannun jari a kamfaninsa karo na biyu a wannan makon, inda suke fatan hannun jarin kamfanin zai kara daraja.

Kara karanta wannan

'Yar aiki ta yi awon gaba da kudi da sarkan N13.9m bayan mako daya kacal da fara aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel