An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

  • An yankewa shugaban makaranta hukuncin shara filin kwallo kan laifin almundahanar kudin makaranta
  • Wata wakiliyar makarantar ta shigar da shi kotu don a kwato kudaden da ya wawure
  • Kotu ta bukaci ya dawo bayan watanni uku bayan sharan filin kwallon Abubakar Tafawa Balewa

Wata kotun majistare dake zamanta a Bauchi ta yankewa wani malamin makaranta hukuncin sharen filin kwallon Abubakar Tafawa Balewa Stadium tsawon watanni uku.

An kama malamin mai suna Abraham Owen da laifin sace kudi N145,000 na makarantar Alfijir Wisdom Academy, dake Bauchi inda ya rike kujeran shugaban makaranta daga 2017 zuwa 2019.

Fatima Shuaibu, ta shigar da kararshi ranar 2 ga Yuni, 2020, rahoton TheCable.

An gurfanar da shi kan laifuka uku wanda suka hada da yaudara, cuta, da almundahana.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige

ABS Kaduna
An yankewa Hedmasta hukunci share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta Hoto: ADS Kaduna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkali mai shari'a, Sadiya Salihu, a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, ta ce bayan binciken da aka gudanar, an kama Malamin da laifi.

An bashi umurnin biyan Fatima Shuaibu kudi N150,000, fiye da N145,000 da ya sata.

Kotun tace ya kamata a tsareshi amma an barshi saboda ya samu daman neman kudin saboda an koreshi daga aiki kuma yanzu bashi da aikin yi.

Kotun ta bashi umurnin aikin share filin kwallo karkashin kulawar jami'a kuma ya dawo kotu bayan watanni uku, ranar 22 ga Maris, 2022.

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Wani mai niyyar takara a zaben shugaban kasa a 2023, Mista Tanimu Audu, ya yi alkawarin kawar da karuwanci inda har yan Najeriya sun zabeshi ya zama shugaba.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: An kamo matar makashin Hanifa, an kai ta kotu, amma ta musanta komai

Audu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai ranar Laraba jihar Bauchi, rahoton TheSun.

Ya bayyana cewa babban dalilin da ke jefa yan mata harkar karuwanci shine rashin aikin yi kuma gwamnati bata sama masu yadda zasu yi da rayuwarsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel