Kotu Ta Yi Hukunci game da Shari'ar Neman Tuge Ɗan Takarar Gwamnan APC
- Babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yi watsi da ƙarar Mustapha Maihaja kan nasarar Baba Wali a zaɓen fidda gwani na APC
- Maihaja ya zargi zaɓen fidda gwani da samun matsalar ƙuri’u fiye da masu zaɓe da karya dokokin jam’iyyar
- Mai shari’a Fatima Amin ta ce an shigar da ƙarar ne bayan wa’adin da doka ta tanada, sannan wanda ya shigar da ita ya kasa gabatar da hujjoji masu ƙarfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Damaturu, Yobe - Wata babbar kotun tarayya da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta yi watsi da ƙarar da Mustapha Maihaja ya shigar domin ƙalubalantar zaɓen Baba Wali a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na APC a zaɓen 2027.
Maihaja, wanda ya fafata da Wali a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar da aka gudanar ranar 21 ga Mayun 2026, ya garzaya kotu yana zargin an tafka maguɗi da wasu kura-kurai yayin gudanar da zaɓen.

Source: Facebook
Daga cikin abubuwan da ya ƙalubalanta akwai zargin ƙuri’u fiye da adadin masu zaɓe da kuma karya ƙa’idojin da APC ta tsara domin gudanar da zaɓen fidda gwani, cewar Punch.
Sai dai a hukuncin da ta yanke ranar Litinin, Mai shari’a Fatima Amin ta amince da ƙin amincewa da shigar da ƙarar bisa hujjar cewa wanda ya shigar da ita ya wuce wa’adin da doka ta tanada.
Dalilin da ya sa kotu ta yi watsi da ƙarar
Mai shari’ar ta bayyana cewa an shigar da ƙarar ne bayan lokacin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada, saboda haka kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.
Ta ce:
“Ba a shigar da wannan ƙara cikin wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada ba. Saboda haka, wannan kotu ba ta da hurumin sauraron batun, domin an shigar da ƙarar ne bayan wa’adin doka.”
Baya ga wannan matsala ta wa’adin shigar da ƙara, kotun ta kuma duba hujjojin da Maihaja ya gabatar kan zargin samun ƙuri’u fiye da masu zaɓe.
Mai shari’a Amin ta ce wanda ya shigar da ƙarar bai gabatar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da zarginsa ba.
Ta bayyana cewa zargin da ake yi, ko da kuwa yana da girma, dole ne a tabbatar da shi da sahihan hujjoji, cewar Vanguard.
Haka kuma, ta gano saɓani da rashin daidaito a bayanan shaidun da Maihaja ya gabatar, lamarin da ta ce ya rage amincin shaidun.
A cewarta, kotu ba za ta iya dogaro da irin waɗannan bayanai masu cike da saɓani wajen amincewa da buƙatun wanda ya shigar da ƙarar ba.
Baba Wali ya samu nasara a kotu
Mai shari’ar ta ƙara da cewa ko da a ce Maihaja ya shigar da ƙarar a cikin wa’adin da doka ta tanada, da wuya ya yi nasara saboda gazawarsa wajen tabbatar da zargin da ya gabatar.
Baba Wali ya samu tikitin takarar gwamnan Yobe na APC ne bayan ya lashe ƙuri’u 236,711 a zaɓen fidda gwani da aka gudanar ranar 21 ga Mayun 2026
Matsalar da za a iya samu a Yobe
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa jam’iyyar APC a Jihar Yobe za ta yi zaben ƙato bayan ƙato idan har ba a cimma matsayar bai-daya kan dan takara ba.
Masu neman takarar gwamna shida sun yi watsi da zaman sulhu da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka yi na tsayar da Alhaji Baba Wali matsayin ɗan takara.
Gwamnan ya nanata cewa hadin kan jam’iyyar shi ne babban burinsa, kuma za su ci gaba da tattaunawa da wadanda zabin Wali bai yi wa daɗi ba don neman mafita.
Asali: Legit.ng


