'An Harbi Motar Atiku Abubakar da Ya Je Kamfen,' Sanata Dino Melaye

'An Harbi Motar Atiku Abubakar da Ya Je Kamfen,' Sanata Dino Melaye

  • Sanata Dino Melaye ya bayyana kalubalen da 'yan jam'iyyar ADC ke fuskanta a Najeriya yayin da aka fara kamfen din zaben 2027
  • Melaye ya yi ikirarin cewa wasu mutane sun kai masu hari da suka je kamfen Sokoto, har an harbi motar dan takarar shugaban kasarsu
  • Melaye ya kara da cewa suna shirye shiryen ganin sun yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027 duk da kalubalen da suke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar ADC, Sanata Dino Melaye ya bayyana kalubalen da 'yan adawa ke fuskanta a Najeriya game da zaben 2027.

Dino Melaye ya bayyana cewa taron da suka yi a Sokoto ya nuna cewa Atiku Abubakar ne zai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

Yadda APC za ta karya lagon Peter Obi a zaben 2027

Dino Melaye a wajen taro
Sanata Dino Melaye na ADC. Hoto: Dino Melaye
Source: Facebook

Melaye ya yi bayanin ne a wani bidiyo da DCL Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook bayan hira da Sanatan game da siyasar Najeriya.

Zargin kai wa Atiku Abubakar hari

Dino Melaye ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar da sauran 'yan ADC na fuskantar barazana a daga wasu mutane.

Ya ce duk wajen da 'yan ADC suka fita kamfen domin neman jama'a ko dai a harbe su da bindiga ko kuma a jefe su da makami.

Sanata Melaye ya ce:

"A wannan tafiyar da aka yi an harbi motar Atiku. Motocin mu guda shida da harsashi aka harbe su."

Dino Melaye ya bayyana cewa yana da bidiyon da aka dauka yayin da aka kai masa hari a wajen taron da suka yi a Sokoto.

Maganar Nafiu Bala da ADC

Game da rikicin da ake da Nafiu Bala da ADC, Dino Melaye ya ce Nafiu Bala ba dan ADC ba ne a halin yanzu saboda ya yi murabus.

Kara karanta wannan

'Babu zaben 2027 matukar aka hana Atiku takara,' Dino Melaye ya yi gargadi

Ya ce duk taron jam'iyyar da aka yi ya nuna cewa Nafiu Bala ba asalin dan jam'iyyar ba ne, saboda haka ya ke mamakin yadda aka ce ya yi nasara a kotu.

Atiku Abubakar da su Abba Hikima
'Yan Tinubu Must Go da suka ziyarci Atiku Abubakar. Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Melaye ya ce an murde masa zaben kogi

Game da zaben Sanata da Dino Melaye ya fadi a 2019, Dino Melaye ya bayyana cewa ya yi nasara a kananan hukumomi shida amma aka murde zaben.

Ya ce lamarin ya samo asali ne daga wani sabani da ya taba samu da marigayi shugaba Muhammadu Buhari a majalisar dattawa.

Haka zalika a zaben gwamnan jihar Kogi da ya shiga aka fafata da shi, ya yi ikirarin cewa shi ne ya ci zaben amma aka juya shi.

Duk da haka, Melaye ya ce a wannan karon kam ba za su yarda a murdewa Atiku nasarar da ake ganin zai samu a zaben shugaban kasa na 2027 ba.

Isa Pantami zai shiga Gombe

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa zai shiga jihar Gombe a ranar Laraba, 11 ga Nuwamban 2026.

Pantami zai shiga jihar Gombe ne a karon farko bayan hukumar zabe ta INEC ta wallafa sunan shi a cikin 'yan takarar 2027.

Sheikh Pantami ya yi kira ga dukkan magoya bayan shi da al'ummar jihar Gombe da su fito su tarbe shi, inda ya ce yana godiya ga jama'ar da suka masa addu'a.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng