"Na Kara Gane Rayuwa," Sanata Ya Dauko Muhimman Darussa a Zaman da Ya Yi a Gidan Yari

"Na Kara Gane Rayuwa," Sanata Ya Dauko Muhimman Darussa a Zaman da Ya Yi a Gidan Yari

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya ce zaman gidan yari ya koya masa darussa da dama tare da sanya shi zama mai tawali’u
  • Tsohon gwamnan Abia ya shafe kusan watanni shida a gidan yari bayan kotu ta same shi da laifi a shekarar 2019, kafin Kotun Koli ta soke hukuncin
  • Ya bukaci ’yan Najeriya da ba su gamsu da hukuncin kotunan kasa ba su daukaka kara zuwa kotunan da suka fi su matsayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa, ya ce bai yi nadamar shafe watanni shida a gidan yari ba bayan da aka same shi da laifi.

Kalu ya bayyana cewa zaman gidan yarin ya ba shi damar koyon darussa da dama tare da kara masa tawali’u.

Kara karanta wannan

Pantami, Fasto Bakare da mutane 5 da suka ki karbar mukamin gwamnatin Tinubu

Kalu.
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Source: Twitter

Sanatan ya yi wannan furucin ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, 2026.

A watan Disambar 2019, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume 39, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari.

Kalu bai yi nadamar zuwa kurkuku ba

Sai dai a ranar 8 ga Mayun 2020, Kotun Koli ta soke shari’ar bayan ta yanke hukuncin cewa alkalin da ya jagoranci shari’ar, Mohammed Idris, ba shi da hurumin yanke hukuncin, saboda an riga an kara masa matsayi zuwa Kotun Daukaka Kara a lokacin.

Kotun Kolin ta bayar da umarnin sake gudanar da shari’ar, daga bisani aka saki Kalu daga gidan gyaran hali na Kuje bayan ya shafe kusan watanni shida a tsare.

Da yake tsokaci kan lamarin, tsohon gwamnan Abia ya ce duk da cewa akwai abubuwan da ake damuwa da su a tsarin shari’a, har yanzu akwai alkalai a manyan kotuna, Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli da ke bin doka yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito bayan shekaru 5, kotu ta sallami wanda ake zargi da kashe matarsa a Kano

“A cikin mutane 12, dole ne a samun guda 1 mai matsala, Har yanzu akwai alkalai masu kyakkyawar fahimta a tsarin shari’a, ko a Babbar Kotun Abuja, ko Babbar Kotun Tarayya, ko Kotun Daukaka Kara, har ma da Kotun Koli."
“Har yanzu akwai masu fahimtar inda ya kamata doka ta tsaya. Don haka, ban yi nadamar ajiye ni a gidan yari ba. Na gode wa Allah sosai, kuma na koyi abubuwa da dama a lokacin da na shafe watanni shida a can.”

- Orji Kalu.

Darussan da Sanata Kalu ya koya

Da aka tambaye shi irin darussan da ya koya daga zaman gidan yarin, Sanata Kalu ya ce abin da ya faru ya sanya shi zama mai tawali’u tare da sauya yadda yake kallon rayuwa.

Ya bayyana cewa zaman gidan yarin ya taimaka masa wajen fahimtar cewa rayuwa ba ta kasancewa yadda mutum yake zato a kowane lokaci.

"Don haka, ina godiya ga Allah da na je can. Ina kuma yabawa mutanen da suka kai ni wurin, domin abin ya kasance kamar zuwa makaranta ne. Na yi karatu a can, kuma na kammala karatuna. Ina matukar farin ciki da na je can,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Atiku: Dino Melaye ya bada labarin yadda kotu ta kira lauyoyin ADC karfe 11:00 na dare

Kalu ya yi hasashen nasarar Tinubu

Kun ji cewa tsohon gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 da gagarumar nasara.

Kalu, wanda a yanzu yake shugabantar kwamitin Majalisar Dattawa kan Hukumar Raya Kudu maso Gabas, ya kare gwamnatin Tinubu daga sukar da ake yi mata kan tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262