Tsohon Gwamna Ya Samu Babban Mukami a Kebbi, Nasir Idris Ya Shirya Wa Zaben 2027

Tsohon Gwamna Ya Samu Babban Mukami a Kebbi, Nasir Idris Ya Shirya Wa Zaben 2027

  • Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC tare da naɗa tsohon gwamna a matsayin jagora
  • Idris ya buƙaci mambobin kwamitin su haɗa kai wajen neman goyon bayan jama’a domin tabbatar da nasarar APC a dukkan muƙaman zaɓe
  • Tsohon gwamnan ya gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa, inda ya sha alwashin yin aiki tuƙuru domin ganin APC ta yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi – Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya naɗa tsohon gwamnan jihar kuma jakadan Najeriya a ƙasar Turkiyya, Saidu Usman Nasamu Dakingari mukami.

Nasir Idris ya nada Dakingari ne a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na shekarar 2027.

Gwamna Idris ya nada Dakingari mukami a Kebbi
Gwamna Nasir Idris na Kebbi, tsohon gwamna Saidu Dakingari da wasu jami;an gwamnati. Hoto: @KBStGovt.
Source: Twitter

Gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin ne a Birnin Kebbi, inda ya buƙaci mambobinsa su yi aiki tuƙuru domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2027, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta ragargaji APC kan hukuncin rusa takarar Atiku a kotu

Idris ya shawarci mambobin kwamitin kan haɗa kai

A yayin ƙaddamar da kwamitin, Idris ya buƙaci mambobinsa su nuna jajircewa, sadaukarwa da ƙwazo wajen wayar da kan jama’a da neman goyon bayansu ga APC a faɗin jihar.

Ya bayyana Kebbi a matsayin jihar da APC ke da ƙarfi, tare da kira ga shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki da su koma yankunansu domin gudanar da gangamin neman ƙuri’u.

Gwamnan ya ce babban aikin kwamitin shi ne tabbatar da nasarar APC a dukkan muƙaman da ake takara, tun daga shugaban ƙasa zuwa kujerun gwamnoni da na majalisun dokoki.

Ya ce:

“Na samu girma da damar ƙaddamar da wannan kwamitin yaƙin neman zaɓe na babban zaɓen 2027, wanda tsohon gwamnan Kebbi kuma jakadan Najeriya a Turkiyya, mai girma Saidu Usman Nasamu Dakingari, zai jagoranta, ina yi wa dukkan mambobin kwamitin fatan alheri.”

Ya kuma bukaci mambobin kwamitin su yi aiki tare domin ci gaba da tabbatar da nasarar APC a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya tarairayi Naira ta dawo hayyacinta, ya kare manufofinsa

Shugaban APC na Kebbi ya yabawa gwamnan

A nasa jawabin, shugaban APC na jihar, Abubakar Kana-Zuru, ya yabawa gwamna Idris bisa goyon bayan da yake bai wa jam’iyyar da kuma ƙoƙarin ƙarfafa tsarinta gabanin zaɓen 2027.

Kana-Zuru ya buƙaci mambobin kwamitin su kasance masu kishin aikin da aka ɗora musu, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da kyakkyawan tsarin gudanarwa.

Dakingari ya yi alƙawarin tabbatar da nasarar APC

Da yake mayar da jawabi, Dakingari ya gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa da sauran mambobin kwamitin.

Ya tabbatar wa Idris cewa za su yi aiki tare da himma domin ganin APC ta samu nasara a babban zaɓen 2027.

Gwamna Idris ya nada Dakingari mukami

A baya, an ji cewa tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Dakingari ya samu babban mukami daga Gwamna Nasir Idris a hukumar alhazai da ke jihar.

Gwamna Nasir ya nada Dakingari mukamin Amirul Hajji na wannan shekara da muke ciki domin kula da jigilar mahajjata.

Gwamnan ya kuma nada Umar Abubakar a matsayin mataimakin Amirul Hajji da kuma Alhaji Malami Shekare-Muhammad a matsayin sakatare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.