Tinubu ne zai ci: Malamin addini ya yi hasashen zaben 2023

Tinubu ne zai ci: Malamin addini ya yi hasashen zaben 2023

  • Gabannin babban zaben 2023, babban faston kasar, David Oyediran, ya yi hasashen cewa babban jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara a zaben
  • Oyediran ya ce Allah ya nuna masa cewa Tinubu zai farfado da kasar sannan ya bunkasa tattalin arzikinta
  • Ya kuma ce duk wasu hasashe da yayi a baya sun faru sun wuce

Shugaban cocin superintendent of Glorious Vision World Outreach Ministries, Rev (Dr.) David Oyediran, ya yi hasashen cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci Najeriya.

A cewar faston, Tinubu na daya daga cikin yan tsirarun mutane da za su iya gyara kasar a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ne zai ci: Malamin addini ya yi hasashen zaben 2023
Tinubu ne zai ci: Malamin addini ya yi hasashen zaben 2023 Hoto: Progressives for Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

A watan nan ne dai tsohon gwamnan na Lagas ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Bakar wahala: Fasto ya hango irin bala'in da 'yan Najeriya za su shiga a 2022

Oyediran a jawabinsa mai taken ‘Nufin Allah kan Najeriya’, ya ce Allah ya nuna masa hakan ne bayan yiwa kasar gagarumin addu’a, The Nation ta rahoto.

A cewarsa:

“Allah ya bayyana cewa a cikin yan tsirarun mutanen da za su iya jagoranci da dawo da muradin yan Najeriya shine Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
“Allah ya ce zai jagoranci Najeriya bisa kundin tsarin mulki kuma zai inganta tattalin arzikin kasar.
“Allah ya kuma fada mani wasu sakonni na sirri zuwa ya Asiwaju Tinubu wanda za su jagorance shi da taimaka masa wajen cika nauyin da Allah zai daura masa kan Najeriya idan jam’iyyarsa ta zabe shi a matsayin dan takararta.”

Oyediran ya magantu kan hasashensa na baya wanda duk sun faru

Da yake tuna hasashensa na baya da suka zama gaskiya, Oyediran ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

"Wasu shekaru da suka wuce lokacin da Cif Michael Otedola ya yi takarar gwamnan jihar Lagas a karkashin jam'iyyar NRC, Ubangiji ya nuna mani cewa Cif Otedola zai yi nasara a zaben kuma ya zama gwamnan jihar Lagas.
"Mutane da yawa basu yarda ba saboda manayn yan siyasan da ke bayan Cif Dapo Sarumi da Farfesa Agbalajobi na jam'iyyar SDP wadanda suma suke takara.
"A karshen zaben, maganar Allah ya afku kamar yadda aka sanar mani sannan Cif Michael Otedola ya lashe zaben ya zama gwamnan jihar Lagas."

Ya kuma ce a 1993 Allah ya bayyana masa cewa MKO Abiola zai lashe zabe sannan za a soke shi, kuma hakan ya faru.

Shugaban kasa a 2023: Ministan Buhari ya bayyana matsayinsa kan tsayawa takarar kujerar

A gefe guda, ministan kwadago da daukar ma'aikata, Sanata Chris Ngige, ya ce yana kan tattaunawa da shugabannin siyasa kuma zai ayyana aniyarsa a kan zaben shugaban kasa na 2023 zuwa lokacin bikin Ista.

Kara karanta wannan

Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun 1997

Ministan ya bayyana hakan ne a ofishin ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya da ke Awka a karshen mako a lokacin da ya ke bayar da tallafi ga mambobin jam’iyyar All Progressives Congress a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel