MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)

MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)

Mai wasan barkwanci, Obinna Simon, wanda aka fi sani da 'MC Tagwaye', ya angonce da amaryarsa Hauwa, diyar Maryam Uwais, mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin jin dadin 'yan kasa.

Da safiyar ranar Lahadi ne Maryam Uwais, uwar amarya, da kanta ta yada hotunan bikin MC Tagwaye da Hauwa a shafinta dandalin sada zumunta.

"A yau ne diyata, Hauwa, ta yi aure. Na yi sabon da, MC Tagwaye. Za su kasance cikin soyayya, raha da barkwanci duk inda suka samu kansu, daga nan har zuwa karshen rayuwarsu.

"Ina neman ku taya wadannan sabbin ma'aurata murna da addu'a. Aure ba abu ne mai sauki ba. Amma addu'arku da taimakon Ubangiji zai taimakesu a cikin rayuwarsu ta aure," a cewarta

Da yake magana a shafinsa na dandalin sada zumunta ranar Asabar, ango MC Tagwaye ya rubta: "wannan rana ta kasance mai muhimmanci, mun dora daga wurin da muka tsaya. Ga masu tambaya, an daura mana aure a yau."

MC Tagwaye ya fara shiga bakin 'yan Najeriya bayan ya kwaikwayi murya da salon zancen shugaba Buhari domin gabatarwa da 'yan Najeriya jawabi amadadin shugaban kasa.

Mai wasan barkwancin, dan asalin jihar Anambra, ya ce ya kasance malamin makaranta da ke samun 'yan karin 'yan kudade daga wasan barkwanci bayan albashinsa..

"Na kasance malamin makaranta na tsawon shekaru fiye da bakwai. Ina koyarwa, ina gwada wasan barkwanci domin tallafawa albashin da nake samu. Ba shugaba Buhari kadai nake kwaikwaya ba.

DUBA WANNAN: Maryam Abacha ta fusata, ta yi tambayoyi a kan kudaden da aka dawo da su Najeriya da sunan mijinta ya sace

"Ina kokari sosai wajen ganin cewa na kwaikwayi kowanne mutum ba tare da samun banbanci mai yawa ba.

"Yanayi da salon maganar Buhari sun fi zama a jikina sosai har ma na kasa komawa yadda nake tun asali.

"Hatta shugaba Buhari takatsantsan yake yi wajen magana lokacin da na ziyarce shi, saboda ba ya son ya fadi wani abu da zan kara rikewa na cigaba da kwaikwayonsa.

"Duk masu kaunar Buhari suna kaunta, haka makiyansa ma sun tsaneni," kamar yadda MC Tagwaye ya shaidawa BBC.

MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)
MC Tagwaye da Hauwa Uwais
Asali: Twitter

MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)
MC Tagwaye da amaryarsa Hauwa Uwais
Asali: Twitter

MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)
MC Tagwaye da Hauwa Uwais
Asali: Twitter

MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)
MC Tagwaye da amarya Hauwa Uwais
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng