Tsoron mutuwa: Yadda attajirai ke zuba kudi don samar da injin da zai sa su tabbata a duniya

Tsoron mutuwa: Yadda attajirai ke zuba kudi don samar da injin da zai sa su tabbata a duniya

  • Ba wanda ke son mutuwa duk da dole ne a mutu, amma manyan attajirai sun yi imanin cewa za su iya dawowa bayan mutuwa inda suke kashe biliyoyin don tabbatar da manufarsu
  • A Turai da Amurka, kamfanoni da kungiyoyi suna karbar kudade duk shekara don daskararwa, da fatan masana kimiyya za su iya gano hanyar tada matattu
  • Ana kashe sama da Naira miliyan 95 duk shekara don hana gawarwaki rubewa, duk da cewa binciken tabbata a duniya har yanzu bai kammala ba

Amurka - Manyan attajirai suna daskarar da gawarwakinsu domin nan gaba su iya tashi, kuma a shirye suke su ba da gudummawar kudade don taimaka wa masana kimiyya su dawo da su bayan sun mutu.

An bayyana cewa dubban daruruwan daloli a kowace shekara ake kashewa a binciken yadda za a tsawaita rayuwa duk da cewa masana kimiyya ba su da tabbacin hakan zai iya faruwa.

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Yadda masu kudin duniya ke zuba kudi a kirkiri injin da zai sa su tabbata a duniya
Karshen duniya: Yadda masu kudin duniya ke zuba kudi a kirkiri injin da zai sa su tabbata a duniya | Hoto: Veejay Villafranca
Asali: Facebook

Daya daga cikin manyan masu goyon bayan wannan aikin shine wanda ya kafa kamfanin Oracle, Larry Ellison wanda aka ruwaito yana ba da dubban daruruwan daloli a shekara a aikin tsawaita rayuwa.

Wadanda suka kafa kamfanin Google, Larry Page da Sergey Brin suma an ba da rahoton sun sanya miliyoyi a kamfaninsu na fasahar kere-kere mai suna Calico, wanda ke kokarin yaki da tsufa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi imanin cewa, manyan attajirai suna da manufar a nan gaba za a iya ta da su domin ci gaba da rayuwa. Kuma hanyoyin da suka zaba don cimma wannan buri shine fasahar Cryonics.

Mene ne Cryonics

Kididdigar kimiyyar da ake magana a kanta ta Cryonics za a iya fahimtar ta kamar haka: kamar dai yadda za ku iya sayen danyen naman saniya a kasuwa ku ajiye a firji saboda kada ya lalace don amfanin gaba, haka suke so nan gaba idan an samu mafita su tashi bayan mutuwa.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

Wane kamfani ne ke aikin kuma nawa ake kashewa?

Alcor Life Extension Foundation wani kamfani ne a kasar Amurka wanda ya yi fice a kasuwancin adana gawarwaki tare da fatan za a iya ta da su nan gaba.

Kamfanin ya fara aikin daskarar da mutane tun a shekarun 1970, kuma akan karbi ya kai kusan Naira miliyan 95.45 (£170,000). Mafi arha shine adana kai kadai.

Ana kashe wadannan kudaden domin ajiye gawarwakin a cikin wata na'urar da za ta daskarar da jiki na tsawon lokaci.

A wani sashen ma, kamfanin cryonics na kasar Rasha wato KrioRus yana ba attajirai zabin daskare dabbobin su tare da su.

Burin mutane kada su mutu

Dokta Roman Bauer, masanin kimiyyar lissafi da kwakwalwa a jami'ar Newcastle ya magantu kan biyan kudin daskarar da jikinsa, inda ya ce:

"Idan da ni mai wadata ne, tabbas zan yi hakan, ko da kuwa damar kashi daya cikin dari ne na yiwuwar aikin cryonics, a haka dai ya fi babu. Amma saboda ba ni da wadata, ba zan yi ba.’

Kara karanta wannan

Ustazai: Wankan kamala na amarya da ango a wajen liyafar aurensu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta

Kalli bidiyon duniyar Cryonics a kasa:

A wani labarin, Daniel Maegaard a da yana samun Naira 6,500 kacal a kowane awa idan ya yi aiki a wani gidan mai a karshen mako yayin da yake karatun ilimin halayyar dan adam a wata Jami'ar.

Maegaard ya kasance yana tara kwabban crypto yayin da yake hada aikinsa da karatu amma gogewa a fannin fasaha da sa'ar rayuwa sun sa ya zama hamshakin attajirin dare daya.

Ya yi tuntube da wani tsagin duniyar crypto da ake kira Non Fungible Tokens (NFTs) shekaru kafin su zama abin da suke yanzu. Wannan ya ba shi damar zama miloniya a cikin shekaru goma da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel