Rikici kan Kayan Mata: Kotu ta bayar da belin Jaruma mai Kayan Mata

Rikici kan Kayan Mata: Kotu ta bayar da belin Jaruma mai Kayan Mata

  • Alkalin wata kotu da ke yankin Zuba a Abuja ya bayar da belin Hauwa Muhammad Sa'idu, wacce aka fi sani da Jaruma mai Kayan Mata
  • Fitaccen biloniya, dan kasuwa kuma dan siyasa, mijin jarumar Nollywood, Regina Daniels ne ya maka ta a kotu kuma aka aike ta gidan yari
  • Sai dai alkali Abdullahi na kotun ya ce aike ta gidan yarin ba ladabtarwa bane, hanya ce da za ta samu saukin ansa tambayoyin da za a yi mata

Zuba, Abuja - Fitacciyar mai siyar da kayan mata, Hauwa Muhammad, wacce aka fi sani da Jaruma, ta shaki iskar 'yanci bayan alkali ya bayar da belin ta.

Jaruma ta gurfana a gaban wata kotu da ke yankin Zuba a Abuja ranar Litinin kan zargin ta da bata suna, wallafar karya tare da cin zarafin fitaccen dan kasuwa kuma biloniya, Ned Nwoko, a kafar sada zumuntar zamani.

Kara karanta wannan

Kakakin PDP ya gurfana a gaban kotu kan caccakar gwamnan APC a Facebook

Rikici kan Kayan Mata: Kotu ta bayar da belin Jaruma mai Kayan Mata
Rikici kan Kayan Mata: Kotu ta bayar da belin Jaruma mai Kayan Mata. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Ned Nwoko ya zargi Jaruma da wallafa karya a shafin ta na Instagram a kan shi da matarsa jaruma Regina Daniels.

Alkalin Ismaila Abdullahi a ranar Litinin ya yanke hukuncin cewa a adana ta gidan gyaran hali na Suleja har zuwa ranar Juma'a da za a yanke hukunci a kan belin ta.

A yayin zaman kotun a yau Juma'a, Jaruma ta bayyana a farfajiyar in mayafi wurin karfe 11 da minti ashirin na safe, Daily Nigerian ta ruwaito.

A yayin yanke hukunci a kan belin, Abdullahi ya ce kada a duba adana ta da aka yi gidan gyaran hali a matsayin ladabtarwa.

Sai dai, ya ja kunnen dukkan wadanda lamarin ya shafa da su kiyaye daukar wani mataki da za a dube shi da yin kai.

Kara karanta wannan

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ya ce:

"Kotun ba ta tsare wacce ke kare kanta ba a matsayin hanyar ladabtarwa, sai dai hanyar da za ta bayyana domin ansa tambayoyin ta. Daga hakan, na ke son hanzarta sanar da cewa zargin da ake wa mai kare kantan za a iya bayar da beli a kan shi.
"A don haka na ke bayar da belin ta bayan ta cika sharudda kamar haka: Tsayayye wanda ke mataki na 12 a aikin gwamnati kuma ya ke aiki a babban birnin tarayya. Sannan dukkan wadanda lamarin ya shafa su guje wa daukar wani mataki."

Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar nan.

Ned Nwoko ya sake sa an cafke Jaruma mai Kayan Mata, alkali ya aike ta gidan yari

A wani labari na daban, fitacciyar mai siyar da kayan mata mai suna Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta shiga gagarumar matsala da biloniyan dan kasuwa, Ned Nwoko.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Sa'o'i kadan kenan da mai siyar da kayan matan ta gama ciki baki kan yadda ta san mutane da kuma kafar da ta ke da ita saboda yadda aka sake ta bayan Ned ya sa an damke ta.

Kamar yadda rahotanni suka tattaro, an sake kama mai siyar da kayan matan a yanar gizo kuma alkali ya aike ta gidan yarin da ke Suleja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel