Ned Nwoko ya sake sa an cafke Jaruma mai Kayan Mata, alkali ya aike ta gidan yari

Ned Nwoko ya sake sa an cafke Jaruma mai Kayan Mata, alkali ya aike ta gidan yari

  • Jaruma ta gigita kafar sada zumunta ta Instagram da cika baki kan yadda ta ke da kafa da kuma yadda ta san mutane saboda sakin ta da aka yi bayan Ned Nwoko ya sa an kama ta
  • Biloniya Ned Nwoko ya sa an sake cafke mai siyar da kayan matan kan zargin ta da ya ke da cin zarafi a yanar gizo, bata masa suna da sauran laifuka da ake zargin ta da su
  • Kamar yadda rahotanni suka bayyana, alkali ya hana lauyan Jaruma belin ta kuma an aike ta gidan yari har zuwa ranar Juma'a, 28 ga watan Janairun 2022

Abuja - Fitacciyar mai siyar da kayan mata mai suna Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta shiga gagarumar matsala da biloniyan dan kasuwa, Ned Nwoko.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Sa'o'i kadan kenan da mai siyar da kayan matan ta gama ciki baki kan yadda ta san mutane da kuma kafar da ta ke da ita saboda yadda aka sake ta bayan Ned ya sa an damke ta.

Bayan sa'o'i da cika baki, Biloniya Ned Nwoko ya sake sa an cafke Jaruma mai Kayan Mata
Bayan sa'o'i da cika baki, Biloniya Ned Nwoko ya sake sa an cafke Jaruma mai Kayan Mata. Hoto daga @nednwoko, @jaruma_empire
Asali: Instagram

An sake kama Jaruma kan zargin bacin suna

Kamar yadda rahotanni suka tattaro, an sake kama mai siyar da kayan matan a yanar gizo kuma alkali ya aike ta gidan yarin da ke Suleja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin abubuwan da ake zargin ta da su sun hada da cin amana, bacin suna, cin zarafi ta yanar gizo da sauran su.

Za a bincike ta kan wasu laifuka, siyar da kayan mata marasa lasisi, siyar da miyagun kwayoyi da sauran su.

An gano cewa, lauyan Jaruma ya bukaci a bayar da belin ta amma kotun ta hana inda ta aika ta gidan yari har zuwa ranar Juma'a mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ango ya danƙara wa amarya saki a liyafar bikinsu kan waƙar da ta zaɓa a saka mata

Amma kuma, asalin shari'ar an dage ta zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da matarsa, Nerita Ezenwa, masoyiyar sa, a ranar Lahadi sun halarci taron haska shirin fim din tarihin rayuwar Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi.

An zabi mutane 200 don halartar taron haska fim din mai suna ‘Yahaya the White Lion’ ma’ana ‘Yahaya farin Zaki’ a Transcorp Hilton da ke Abuja, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel