Kwastam sun hama Hodar Iblis ta Biliyan N3.9 a wata mota dake ɗakko litattafan Addini

Kwastam sun hama Hodar Iblis ta Biliyan N3.9 a wata mota dake ɗakko litattafan Addini

  • Jami'an hukumar Kwastam dake aiki a Seme da Badagry sun cafke wata motar ɗauko litattafan addini ta ɗauko Hodar Iblis
  • Kakakin kwastam, Hussaini Abdullahi, yace jami'an sun gano cewa Hodar ta kai darajar Naira Biliyan N3.9bm
  • Yace jami'an sun kuma kama Man fetur da akai safarar shi ba bisa ka'ida ba da yakai jarka sama da dubu ɗaya

Lagos - Hukumar kwastan reshen Seme, jihar Legas, tace jami'anta sun damƙe wata motar Bas dake ɗakko litattafan Addini ɗauke da Hodar Iblis mai nauyin 11.913.

A cewar hukumar Hodar da jami'an suka kama ta kai darajar kuɗi kimanin Biliyan N3.9bn, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kakakin hukumar reshen Seme, Hussain Abdullahi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Kwastam
Kwastam sun hama Hodar Iblis ta Biliyan N3.9 a wata mota dake ɗakko litattafan Addini Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Ya ce jami'an sun yi ram da jarkokin man fetur da aka jera a cikin buhuna, duk a wani bangare na yaƙi da safarar kayayyaki ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje a jihar Kano ya ɓace

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Pumch ta rahoto Yace:

"Jami'an kwastam sun fara Sintiri na musamman kan masu safarar man Fetur ba bisa ƙa'ida ba a yankunan Seme da Badagry. Wannan yunkurin ya yi sanadin kame man fetur da yawa a ranar Laraba 26 ga watan Janiru.
"Bayan gudanar da bincike kan kayan, mun gano akwai jarkoki 1,065 na man fetur, wan da ya yi daidai da Lita 31,950, tare da kuɗin duti N10,041."

Yadda Jami'ai suka kam Hoda

Mista Abdullahi ya kara da cewa yayin da jami'an ke gudanar da aikin binciken ababen hawa a hanyar Seme-Badagry sun kama wani kunshin kaya 11 da suke zargin Hodar Iblis ce.

Jami'an sun kama ƙunshin kayan a wata mota dake ɗakkon kayan litattafai na Addini, kuma tuni aka kama mutum ɗaya dake da hannu a lamarin.

"Bayan gwajin kunshin kayan da hukimar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi (NDLEA) da hukimar NAFDAC suka yi, sun gano Hodar Ibilis mai nauyin Kilo 11.913kg."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe

A wani labarin kuma Shugaba Buhari yace gwamnatinsa na aiki ba ji ba gani don tabbatar da zaman lafiya ya dawo a jihar Zamfara cikin kankanin lokaci

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa da jihar Zamfara na aiki ba ji ba gani wajen tabbatar da zaman lafiya ya dawo jihar.

Shugaban wanda hazo ya hana shi kai ziyarar jaje Zamfara, yace ya baiwa hukumomin tsaro umarnin cigaba da yaƙar yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel