Abin da gwamnatin mu take yi don tabbatar da zaman lafiya ya dawo Zamfara cikin ƙanƙanin lokaci, Buhari

Abin da gwamnatin mu take yi don tabbatar da zaman lafiya ya dawo Zamfara cikin ƙanƙanin lokaci, Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa da jihar Zamfara na aiki ba ji ba gani wajen tabbatar da zaman lafiya ya dawo jihar
  • Shugaban wanda hazo ya hana shi kai ziyarar jaje Zamfara, yace ya baiwa hukumomin tsaro umarnin cigaba da yaƙar yan ta'adda
  • Buhari ya ƙara da cewa cikin ƙanƙanin lokaci zaman lafiya zai samu gindin zama a Zamfara

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace gwamnatinsa na aiki tuƙuru domin tabbatar da zaman lafiya ya samu gindin zama a jihar Zamfara cikin ƙanƙanin lokaci.

The Cable ta rahoto cewa shugaban ƙasa ya shirya zuwa jihar Zamfara ta'aziyya da jaje ranar Alhamis, amma dole tasa aka soƙe tafiyar saboda hazo.

Da yake jawabi ga al'ummar jihar Zamfara ta Talabijin ranar Alhamis da yamma, shugaba Buhari, yace "na yi takaici" rashin zuwa jihar Zamafara.

Kara karanta wannan

Buhari ya aike wa Zamfarawa sakon bidiyo da na rediyo kan fasa ziyararsu da ya yi

Shugaba Muhammadu Buhari
Abin da gwamnatin mu take yi don tabbatar da zaman lafiya ya dawo Zamfara cikin ƙanƙanin lokaci, Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A wata sanarwa da hadimin shugaban, Femi Adesina, ya fitar, Buhari ya ƙara da cewa ya baiwa hukumomin tsaro umarnin cigaba da ƙaddamar da hare-hare kan yan bindiga a faɗin jihar.

Buhari yace:

"Na ji ciwon rashin kasancewa ta da ku (al'ummar Zamfara) yau kamar yadda na shirya. Na kammala abin da ya kaini Sokoto na kamfanin BUA Cement, kuma na shirya zuwa gare ku."
"An faɗa mun cewa tafiyar ba zata yuwu ba saboda rashin kyaun yanayi, sakamakon haka ba zai yuwu Helikwafta na ya tashi zuwa Gusau ba daga Sokoto."
"Na san baku ji daɗin haka ba amma Allah shi ne masani. Na yi matukar jajantawa gwamnan ku da majalisarsa domin sun kammala shirin komai na zuwa na. Na ƙagu yanayi ya yi kyau domin na kawo muku ziyara."

Kara karanta wannan

Zan murƙushe yan ta'adda baki ɗaya kafin na sauka daga mulki, Shugaba Buhari

Wane mataki FG ke ɗauka na dawo da tsaro Zamfara?

Buhari ya ce tuni ya baiwa hukumomin tsaro umarnin cigaba da aikin su ba tare da gajiya wa wajen murƙushe yan ta'adda baki ɗaya.

"Gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya ya dawo cikin ƙanƙanin lokaci."

A wani labarin kuma Cikin jihohi 36, An bayyana gwamnan jihar da ya fi kaunar zaman lafiya a Najeriya

Gidauniyar wanzar da zaman lafiya ta baiwa gwamnan jihar Enugu, lambar yabo ta gwamnan da ya fi son zaman lafiya a Najeriya.

Shugaban gidauniyar, Dakta Sulaiman Adejoh, yace sun yi nazari kan muhimman ayyukan gwamnan kafin su zaɓe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel